Boko Haram Sun Kai Hari Sansanin Sojoji A Borno
[ad_1]
Wani dan ƙunar baƙin wake da ke tuka mota cike da abubuwan fashewa ya kutsa cikin ayarin motocin sojoji a yankin Timbuktu Triangle na Jihar Borno, inda ya yi sanadin mutuwar sojoji biyar tare da jikkata wasu da ba a bayyana adadinsu ba.
Majiyoyin sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce cikin waɗanda harin ya shafa har da manyan jami’an soji biyu masu muƙamin Manjo da kuma Laftanar, tare da haddasa babbar asara ga kayan aikin soja da ake amfani da su wajen kai hare-hare da farmaki da ma kare kai a aikin kawar da ‘yan ta’adda da sojojin suka shafe makonni suna yi.
- Zargin Almundahana: Kwamitin NAHCON Ya Kaɗa Ƙuri’a Kan Neman A Kori Shugabanta
- Jami’an Tsaro 6 Sun Rasu Yayin Da Aka Daƙile Harin ’Yan Ta’adda A Zamfara
Rahotanni sun bayyana cewa sojojin suna kan hanyar dawowa ne daga wani samame da suka yi nasarar tarwatsa sansanonin ‘yan ta’adda da dama tare da kashe da yawa daga cikinsu, lokacin da harin ya auku, inda aka lalata motocin sulke da na kayan aiki.
Yankin Timbuktu Triangle shi ne wurin da a kwanakin baya ‘yan ta’adda suka yi wa ayarin Brigadier Janar Musa Uba kwanton bauna, tare da kama shi inda daga baya kuma suka kashe shi.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba, ya fitar a yayin da ake ci gaba da atisayen wanda ake yi wa laƙabi da Tsaftace Sahara “DESERT SANITY”, ya ce an sun ƙwato makamai da kayan aiki daga hannun ‘yan ta’addan.
Ya jaddada cewa Rundunar Soji na kan aniyarta na ci gaba da wannan aiki, inda sojojin za su ruɓanya ƙoƙarinsu na kawar da ayyukan ta’addanci da kare fararen hula, da kuma dawo da dawwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a Arewa maso Gabas.
[ad_2]
Source link