Masana sun nuna damuwa a Arewa maso Gabas

[ad_1]



Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa kimanin mutum ɗaya cikin kowane mutum 30 na fama da cutar koda a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, inda suka bayyana damuwa kan ƙaruwa masu fama da matsalar a yankin.

Sun kuma bukaci mazauna yankin da su rungumi yin gwajin lafiya akai-akai da kuma rayuwa mai kyau domin rage haɗarin kamuwa da cutar koda.

An bayyana hakan ne yayin wani shirin gwajin lafiya kyauta da Hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabas (NEDC) ta ɗauki nauyi a Jihar Gombe, wanda aka gudanar ga manya da yara.

Likitan yara mai kula da cututtukan koda, Dokta Ali Razak, ya ce manufar shirin ita ce inganta gano cutar da wuri tare da hana ta rikidewarta zuwa mai tsanani.

“Gano cuta da wuri na da matuƙar muhimmanci wajen rage matsalolin da za su biyo baya,” in ji shi.

Likitan ya kuma bayyana cewa yawancin cututtukan koda a yara na farawa tun daga haihuwa, yana mai jaddada bukatar kai yara asibiti da wuri tare da ci gaba da bibiyar lafiyarsu akai-akai.

Hakazalika, ya yi gargadi kan amfani da magunguna ba tare da shawarar likita ba, yana mai cewa hakan na iya lalata ƙoda.

A cewarsa, cututtuka kamar zazzabin cizon sauro, gudawa, cututtukan fata, da rashin isasshen ruwa a jiki na daga cikin manyan abubuwan da ke jawo matsalolin koda a yara.

Ya kuma bukaci iyaye da su tabbatar da ba yara magani yadda ya kamata tare da ba su ruwa isasshe.

“Ga manya kuma, hawan jini da ciwon sukari su ne manyan abubuwan da ke haddasa cutar. Yin gwajin lafiya akai-akai yana da matuƙar muhimmanci,” in ji shi.

Dokta Razak ya bayyana cewa an tsara yin gwaji ga kimanin mutane 150, tare da shirin kula da waɗanda aka gano suna da matsalar.

Shi ma jami’in kula da ayyukan NEDC a jihar, Akitet Usman Mohammed, ya ce shirin na daga cikin ƙoƙarin inganta lafiyar al’umma da faɗaɗa samun kulawar lafiya, musamman ga marasa ƙarfi.

Wasu daga cikin waɗanda suka amfana, ciki har da Vasty Bala da Esther Alhassan, sun bayyana shirin a matsayin wanda ya zo a kan lokaci.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *