Za a soma bai wa raƙuma fasfo a ƙasar Saudiyya
[ad_1]
Gwamnatin Saudiyya ta sanar da shirinta na fara bai wa miliyoyin raƙuman da ke ƙasar fasfo, a wani yunƙuri na inganta kula da su da kuma sauƙaƙa tsarin gudanar da muhimmin fannin kiwon raƙuma.
Ma’aikatar Muhalli, Ruwa da Noma ta ce shirin zai ƙara inganci da kawo ayyuka a fannin, tare da samar da sahihin kundin bayanai da za a riƙa dogaro da shi wajen tantance shaida da mallakar raƙuma.
Wani saƙo da ma’aikatar ta wallafa ranar Talata a shafukan sada zumunta ya nuna hoton fasfon, wanda ke da launin kore, tare da tambarin ƙasar da kuma hoton raƙumi mai launin zinariya.
Ma’aikatar ta ce fasfon zai zama hanyar tantance raƙuma, wadda ke ɗauke da lambar microchip, lambar fasfo, sunan raƙumin, ranar haihuwa, jinsin raƙumi, mace ko namiji, launi, wurin haihuwa, ranar da wurin da aka bayar da fasfon, tare da hotunan raƙumin daga ɓangarori biyu domin tantance ainihinsa.
Fasfon ya kuma ƙunshi shafin bayanan rigakafi na musamman, inda ake rubuta allurar rigakafin dabbobi da aka yi masa, tare da sunan likitan dabbobi, sa hannunsa da hatiminsa..
A shekarar 2024, gwamnatin Saudiyya ta ƙiyasta cewa akwai kusan raƙuma miliyan biyu da dubu dari biyu a ƙasar.
Saudiyya kuma na shirya gasar kyau na raƙuma a lokacin bukukuwan shekara-shekara, lamarin da ke nuna muhimmancin raƙumi a al’adu da tattalin arziƙin ƙasar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link