’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 5 a Bauchi

[ad_1]



Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta tabbatar da mutuwar wasu jami’anta guda biyar a ƙauyen Sabon Sara da ke Ƙaramar Hukumar Darazo, sakamakon harin da wasu ’yan bindiga suka kai.

Kakakin rundunar, CSP Ahmed Wakil ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranae Lahadi.

“‘Yan sanda biyar sun rasu, biyu sun jikkata, amma an yi nasarar kashe wasu daga cikin ’yan bindigar a ƙauyen Sabon Sara, Ƙaramar Hukumar Darazo, a jihar Bauchi.”

Wakil, ya ƙara da cewa, “Ma’aikatanmu suna jajircewa kuma sun samu nasarar kashe wasu daga cikin ’yan bindigar yayin musayar wuta.”

Ya bayyana ’yan sanda suna aikin sintiri lokacin da aka kai musu harin.

Wakil, ya bayyana sunayen ’yan sandan da suka rasa rayukansu; DSP Ahmad Muhammad (SID), ASP Mustapha Muhammad (10 PMF), Amarhel Yunusa (10 PMF), Idris Ahmed (10 PMF), da Kofur Isah Muazu (AKU).

’Yan sandan da suka ji rauni sun haɗa da Isah Musa (SID) da Insifekta Yusuf Gambo (SID).

Ya ƙara da cewa, “Bayan samun rahoton, Shugaban ’yan sandan Ƙaramar Hukumar, SP Auwalu Ilu, ya jagoranci tawaga tare da ceto waɗanda suka jikkata.

“Sun kai waɗanda suka rasu Babban Asibitin Darazo, inda aka ajiye gawarwakin a ɗakin ajiyar gawa.

“Ana ƙokarin kama waɗanda suka aikata wannan mummunan laifi tare da hukunta su,” in ji Wakil.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya ziyarci wajen da lamarin ya faru, sannan miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu.

“Aikin nan ba abu ne mai sauƙi ba. Duk da haka, bisa doka, za mu ci gaba da jajircewa ba dare ba rana don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *