’Yan sanda sun ƙaryata jita-jitar kai wa coci hari a Gombe

[ad_1]



Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta ce labarin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na kai wa cocin ECWA da ke Kashere hari, ba gaskiya ba ne.

Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ne, ya bayyana haka, inda ya ce sun bincika tare da gano cewar jita-jita ce.

Ya ce DPO na Pindiga da shugaban ofishin ’yan sanda na Kashere, sun tuntuɓi wani dattijo da ya halarci cocin domin yin addu’a a ranar Lahadi.

Dattijon ya shaida musu cewa babu wani abu da ya faru, kuma ’yan sanda suna harabar cocin tun safe a domin kula da sha’anin tsaro kamar yadda suka saba.

Rundunar ta ce yaɗa irin wannan jita-jitar na iya tayae da hankalin jama’a.

Ta kuma ce ta fara bincike domin gano wanda ya ƙirƙiri wannan labari domin ɗaukar matakin doka a kansa.

DSP Abdullahi, ya roƙi jama’a da su kwantar da hankalinsu, tare da ci gaba da harkokinsu, inda ya tabbatar da cewa ’yan sanda za su ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *