Mutane 3 Mafi Tasiri A Rayuwar Ƙwallon Ƙafa Ta – Osimhen
[ad_1]
Ɗan wasan gaba na ƙungiyar Galatasaray, Victor Osimhen, ya bayyana wasu manyan ‘yan wasa uku da suka taka muhimmiyar rawa wajen da shi iya ƙwallon ƙafa.
Ɗan wasan mai shekaru 27 ya ambaci tsohon ɗan wasan Ivory Coast, Didier Drogba, da tsohon ɗan wasan Nijeriya, Odion Ighalo, da kuma tsohon kyaftin na Super Eagles, John Obi Mikel, a matsayin waɗanda suka zama abin koyi a gare shi.
- Madrid Da PSG Na Shirin Sayen Osimhen
- Babu Wani Sabani Tsakanin Osimhen Da Lookman – Ndidi
Osimhen ya bayyana hakan ne yayin wata hira kai tsaye a Twitch tare da ɗan barkwanci Carter Efe a safiyar ranar Asabar.
A cewarsa, ya jingina nasarorinsa gaba ɗaya ga Allah, tare da cewa akwai wasu mutane da suka taimaka masa wajen daidaita rayuwarsa da ƙwarewarsa.
“Dangane da ƙwallon ƙafa, kowa ya san ina samun ƙwarin gwuiwa daga Didier Drogba, haka kuma daga irin su Odion Ighalo,” in ji shi.
Ya kuma tuna haduwarsa ta farko da John Obi Mikel lokacin da aka kira shi zuwa tawagar Super Eagles karo na farko.
“Na gan shi bayan mun gama cin abinci, sai na ce masa ‘Senior man, zan zo ɗakinka.’ Sai ya ce in biyo shi nan take,” in ji Osimhen. “Ya gayyace ni zuwa ɗakinsa, sannan ya bani kuɗi. Ba zan iya faɗin adadin ba, amma ya bani kuɗi a fam.”
[ad_2]
Source link