NDLEA Ta Kwace Kwayoyin Pregabalin 75,000 Da Hodar Iblis 556 A Kano

[ad_1]

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta kasa, NDLEA, reshen Kano, ta kama kwayoyin Pregabalin guda 75,000, kwalaben maganin tari mai dauke da Codeine 556, da kuma wasu adadin tabar wiwi (Cannabis satiba) a yankin Badawa na Kano.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Sadik Muhammad-Maigatari, ya fitar a ranar Litinin a Kano.

  • Wang Yi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Ministar Harkokin Wajen Birtaniya
  • Aikin Zamantar Da Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya Zai Rage Wa Kasa Asasar Naira Tiriliyan Daya —Dantsoho

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya, (NAN), ya ruwaito cewa Pregabalin magani ne da ake amfani da shi wajen rage radadi da kuma maganin cutar farfadiya, amma hukumar NDLEA ta ce a cikin ‘yan shekarun nan ya zama daya daga cikin magungunan da ake yawan amfani da su ba bisa ka’ida ba a Nijeriya.

Da yake mayar da martani kan wannan kamen, kwamandan NDLEA a Kano, Dahiru Yahaya-Lawal, ya ce an samu nasarar kwace miyagun kwayoyin ne bayan sahihan bayanan sirri da suka nuna cewa an shirya rarraba su ne a lokacin bukukuwan Eid al-Fitr da ke tafe.

Ya ce, “Wannan samame ya dakile wani babban shiri na rarraba miyagun kwayoyi zuwa kasuwannin haramtattun kwayoyi.”

NDLEA ta kuma bayyana cewa babban wanda ake zargi da hannu a safarar kwayoyin ya tsere, kuma yanzu haka an saka sunansa cikin jerin mutanen da ake nema ruwa a jallo.

“Wannan kamen ya yi wa hanyar sadarwar wannan kungiyar fataucin miyagun kwayoyi babbar illa, kuma ya kare al’ummar Kano daga illolin wadannan kwayoyi,” in ji Yahaya-Lawal.

Ya kara da cewa rundunar za ta ci gaba da bin umarnin shugaban NDLEA kuma babban jami’in gudanarwa na hukumar, Mohamed Buba Marwa, domin tabbatar da an samu al’umma marar miyagun kwayoyi, tare da ci gaba da yaki da sha da fataucin kwayoyi.

Hakazalika, ya yaba wa jama’a bisa ci gaba da ba hukumar hadin kai, tare da rokonsu su rika ba da bayanai masu amfani da za su taimaka wajen dakile safarar miyagun kwayoyi.

Yahaya-Lawal ya kuma gargadi duk masu hannu a harkar safarar miyagun kwayoyi da su daina, yana mai jaddada cewa hukumar ba za ta gajiya ba wajen kamo masu laifi tare da gurfanar da su a gaban doka. (NAN)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *