Majalisar Dattawa ta amince da ƙudirin Dokar Zaɓe ta 2026

[ad_1]



Majalisar Dattawan Najeriya a wannan Talatar ta amince da ƙudirin Dokar Zaɓe ta 2022 da aka yi wa kwaskwarima.

An amince da ƙudirin da a yanzu ya zama Dokar Zaɓe ta 2026 bayan tattaunawa bisa la’akari da tanadin sashe na 155 na dokar.

Aminiya ta ruwaito cewa an yi sauye-sauye a wasu daga cikin sassan dokar, yayin da aka bar mafi yawan hukunce-hukuncen kamar yadda aka gabatar da su tun farko.

Sai dai Majalisar Dattawan ta ƙi amincewa da wani gyara da aka gabatar wa Sashe na 60, Ƙaramin Sashe na 3, wanda ya buƙaci tilasta tura sakamakon zaɓe ta hanyar laturoni kai tsaye daga kowace rumfar zaɓe.

Majalisar ta ce za a ci gaba da amfani da tsarin da ya tanadi cewa jami’an zaɓe na INEC su riƙa tura sakamakon zaɓe kai tsaye daga rumfar zaɓe zuwa manhajar IREV bayan an sanya hannu da kuma buga hatimi a fom ɗin EC8A, wanda kuma zai ƙunshi sa hannun wakilan jam’iyyun siyasa.

Haka kuma, a cikin gyare-gyaren da aka yi wa dokar ta 2022 shi ne rage wa’adin da Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC) ke da shi na fitar da sanarwar zaɓe daga kwana 360 zuwa 180.

Wannan na zuwa ne bayan ƙudirin da Sanata Tahir Monguno ya gabatar, inda ya buƙaci a cire batun tura sakamakon ta laturoni, tare da barin tsohon tanadin yadda yake.

Monguno ya kuma bayyana cewa rage wa’adin kwanakin ya zama dole domin hukumar INEC ta cika sharuɗɗan da ake buƙata wajen fitar da sanarwar, inda ya ce tuni aka makara idan aka yi amfani da kwana 360 bisa la’akari da babban zaɓe mai zuwa.

Majalisar dai ta fuskanci matsin lamba kan abin da wasu suka bayyana a matsayin jan ƙafa wurin amincewa da ƙudirin dokar zaɓen.

Sai dai da yake jawabi bayan kammala karatu na uku, Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ya ce an samu jinkirin ne a ƙoƙarin da suka yi na gudanar da ingantaccen aiki na nazartar dokar cikin tsanaki.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *