2027: APC na cikin tsaka mai wuya kan bai wa ’yan takara tikiti
[ad_1]
Yayin da kakar babban zaɓen 2027 ke ƙara ƙaratowa, jam’iyya mai mulki ta APC ta tsinci kanta a wata tsaka-mai-wuya biyo bayan matsin lambar da mambobinta ke yi na ganin an ba su tikitin takara ba tare da fuskantar zaɓen fidda-gwani ba.
Wannan buƙata, wadda ta fito fili daga ɓangaren ’yan majalisar tarayya, na nufin suna son jam’iyyar ta ba su kariya ta musamman domin komawa kan kujerunsu kai-tsaye.
A gefe guda kuma, wasu gwamnoni masu shirin kammala wa’adin mulkinsu na biyu sun sa ɗamarar ganin sun karɓi tikitin takarar Sanata ba tare da wata fafatawa ba.
Lamarin ya nuna yiwuwar samun babban tsaiko tsakanin masu riƙe da madafun iko a jihohi da na tarayya.
Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya bayyana cewa ba da wannan dama ga ’yan majalisa zai taimaka wajen kiyaye ƙwarewar aiki da kuma tabbatar da daidaito a tsarin gudanar da mulki.
Wannan batu ya samu gagarumin goyon baya daga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wanda ke ganin hakan a matsayin hanya mafi dacewa ta rage yawan sauya fuskoki a majalisar dokoki.
Domin tattauna wannan dambarwa, uwar jam’iyyar ta gudanar da wani taron sirri da kusan mambobi 230 a Abuja kwanan nan, duk da cewar ba a cimma matsaya ta ƙarshe ba.
Amma jam’iyyar ta ba su tabbacin cewa za ta yi dukkanin mai yiwuwa wajen kare muradun mambobinta.
Duk da wannan alƙawari, akwai ɗar-ɗar a zukatan wasu ’yan majalisa wadanda ke fargabar cewa gwamnonin jihohinsu na iya murƙushe burinsu domin karkata kujerun ga kansu ko na-kusa da su.
Wannan taƙaddama ta riga ta fara haifar da rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar APC, inda kowane ɓangare ke ƙoƙarin kare tasa muradin.
Masanin kimiyyar siyasa, Mathew Ifeolu, ya yi gargaɗin cewa idan har ba a bi lamarin cikin masalaha da adalci ba, wannan rikici na iya zama tamkar nakiya ne da ke jiran fashewa, wanda zai iya raba kan jam’iyyar tare da bai wa ’yan adawa damar cin gari a zaɓe mai zuwa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link