Zulum Ya Bayar Da Tallafin Naira Miliyan 150 Ga Iyalan Jami’an Soji Da Suka Rasu.

[ad_1]

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya bayar da tallafin naira miliyan 150 ga iyalan jami’an soji uku da suka rasu—Laftanar Kanal Umar Farouq, Salihu Iliyasu, da Aliyu Saidu Paiko—waɗanda mayaƙan Boko Haram suka kashe a jihar.

Wannan tallafi, a cewar wata sanarwa da Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan kan Harkokin yada labarai, Abdulrahman Bundi, ya fitar a ranar Laraba, wani ɓangare ne na ci gaba da goyon bayan da gwamnan ke bai wa iyalan jarumai da suka rasu da kuma waɗanda suka jikkata yayin yaƙi da ta’addanci a fadin jihar.

“Domin nuna goyon baya da tausayawa ga iyalan da suka yi rashin mazajensu, a ranar Laraba Gwamna Zulum ya kai ziyara ga iyalan marigayi Laftanar Kanal Umar Farouq, Laftanar Kanal Salihu Iliyasu, da Laftanar Kanal Aliyu Saidu Paiko,” in ji sanarwar.

A yayin ziyarar, Gwamnan ya bai wa duk iyalan marigayan cekin kudi na naira miliyan 50 ga kowannensu, da ke zaune a babban birnin tarayya Abuja, Jihohin Neja, da Kano.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *