Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tabbatar Da Hukuncin Kisa Kan Wanda Ya Kashe ‘Yar Shekara 5 A Kano

[ad_1]

Rabiu Ali Indabawa

Kotun Daukaka Kara da ke zama a Kano ta sake tabbatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya da aka yanke wa Abdulmalik Tanko bisa laifin garkuwa da kuma kisan yarinya ‘yar shekara takwas, Hanifa Abubakar.

Mai Shari’a A.R. Muhammad, wanda ya karanta hukuncin a ranar Talata, ya yi watsi da karar da Tanko ya shigar, tare da tabbatar da hukuncin Kotun Babbar Jihar Kano, yana mai cewa kotun shari’ar farko ta yi aiki daidai da doka kuma ta tantance shaidu yadda ya kamata.

  • Gwamnan Gombe Ya Kafa Hukumar Kula Da Wutar Lantarki
  • Buƙatar A Sake Duba Sabuwar Dokar Haraji

A cewar Mai Shari’an, kotun daukaka karar ta gano cewa hujjojin da mai kara ya gabatar ba su da karfi, inda ta ce shaidun da masu kare hukuncin suka gabatar sun kasance masu karfi da gamsarwa.

Saboda haka, ya bayyana cewa babu wani dalili da zai sa a tsoma baki a hukuncin kotun kasa.

Mai Shari’a Muhammad ya kuma yi kira ga gwamnati da ta tabbatar an aiwatar da hukuncin bayan wanda aka yanke wa hukuncin ya kammala dukkan hanyoyin daukaka kara da doka ta tanada.

Rahoton LEADERSHIP ya bayyana cewa Hanifa Abubakar, ‘yar shekara biyar, an sace ta a watan Disamba 2021 da Abdulmalik Tanko, mamallakin makarantar Noble Kids Academy da ke Karamar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano.

Tanko ya nemi kudin fansa Naira miliyan 6 daga iyayenta kafin daga bisani ya sanya mata guba ta bera, abin da ya yi sanadiyyar rasuwarta.

Lamarin ya jawo Allah-wadai daga sassa daban-daban na kasar nan, sakamakon karancin shekarun yarinyar da kuma cin amanar da aka yi, ganin cewa Tanko shi ne mamallakin makarantar da take karatu a cikinta.

An gurfanar da Tanko a gaban kotu a ranar 24 ga Janairu, 2022, tare da Isyaku Hashim da Fatima Jibril, kan tuhuma da suka shafi hada baki wajen aikata laifi, garkuwa da mutane, tsare mutum ba bisa ka’ida ba, da kuma kisan kai da gangan.

A ranar 28 ga Yuli, 2022, Kotun Babbar Jihar Kano, karkashin jagorancin Mai Shari’a Usman Na’abba, ta yanke wa wanda aka samu da laifi da kuma Hashim hukuncin kisa ta hanyar rataya, yayin da aka yanke wa Fatima Jibril hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *