Kisan Gillar Mutum 7 A Kano: Sarakuna Da Malamai Da Iyaye Sun Nemi A Gaggauta Yanke Wa Waɗanda Ake Zargi Hukunci

[ad_1]

Batun Kisan Gillar Da aka wayi gari dashi a Unguwar Chiranci dake yankin Ƙaramar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano, lamari ne da ya tayar wa da Al’umma hankali shi ne yadda batun Kashe kashen Jama’ar ya zama tamkar ruwan dare, sai dai wannan da a halin ya ke dumama hazo ya zama akwai tsananin rashin Imani, cin amana da Kuma tsabar rashin tarbiyyar matasan wannan lokaci.

Duk da kyakkyawan tarihi, yakana da kuma kasancewar Jihar Kano ta yi shura ta fuskar ilimi da kuma wadatar zuci ta fuskar kasuwanci da sana’o’in dogaro da kai amma a waɗannan ‘yan shekaru Jihar ta koma wani dandamalin ba makasa ke baje kolinsu ta yadda ake kashe mutanen da basu ji ba Kuma basu gani ba.

Kisan Gillar Da ya faru ne a Unguwar Chiranci wani lamari ne mai cike da ayoyin tambaya, musamman kasancewar an gudanar da wannan aika aika ne da rana tsakankanin tsakiyar Unguwar da take cike da al’umma, amma waɗannan makasa suka kutsa wannan gida tare da kulle ƙofar shiga gidan sannan suka ci gaba da aiwatar da ta’addancin su, har wasu makwbtan sun bayyana cewa sun ji ihun Matar tana ambaton Umar har da kai za a kashemu?

  • Gobara Ta Ƙone Wani Sashi Na Maƙabarta A Kano
  • Majalisa Ta Yaba Wa ‘Yansanda Kan Gaggawar Kama Waɗanda Ake Zargi Da Kisan Gilla A Kano

Sannan wani abin tambaya shi ne yadda har suka gama kisan wanda su makwabtan suka ce maharani basu fito suma cikin gidan, duk da yadda Jami’an tsaro sun yi amfani da duk wata dama ta yadda aka hau saman gidan ba a same su ba. Wannan almarimn fa ya faru daga misalin ƙarfe 11:00 na safe zuwa Ƙarfe 1 na rana ne zuwa sama.

Maharan sun samu nasarar kashe Uwa da ‘ya’yan ta Shida, wani tsabar rashin tausayi akwai jaririn da suka jefa rijiya, kamar yadda makwabtan wannan gida suka shaida cewa jami’an tsaro sun isa a kan lokaci kuma sun yi bakin ƙoƙari inda aka kwashi gawawwakin zuwa asibitin Murtala inda aka tabbatar mutuwarsu tare da miƙa su ga iyalansu inda aka yi masu sutura kamar yadda addinin Musulumci ya tanada.

Habibu Sharaɗa ya bayyana cewa, tabbas na kaɗu matuƙa da naji an ce Umar shi ne wanda ya aikata wannan kisan, domin bayan an yi kisan misalin ƙarfe uku na rana ya zo wajen mu muka zauna tare da shi muna alhinin mutuwar, har hannun sa na hagu na gani a kumbure nake tambayar sa mene ya same shi? Yake ce min targaɗe ya yi a wajen aiki na ce masa Allah ya sawwake ya kiyaye gaba.

Ya ci gaba da cewa shi wannan Umar ɗin, ita wacce aka kashe jiya tare da ‘ya’yan ta ƙanwar mahaifinsa ce.

Sannan kwanaki kaɗan da suka wuce akwai matar da aka kashe tare da kishiyarta a Tudun Yola ita kuma ƙanwar mahaifiyar sa ce, haka kuma watanni biyar da suka wuce akwai yarinyar da aka ƙwakulewa idanu aka kashe ta a unguwar Sabuwar Gandu, ita kuma ƙanwar sa ce.

Idan za a tuna rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta sanar da cafke mutane uku da ake zargi da hannu a mummunan kisan gilla da aka yi wa wata matar aure da ’ya’yanta shida a unguwar Xorayi Chiranchi da ke cikin Birnin Kano.

A cewar wata sanarwa da rundunar ta fitar, lamarin ya faru ne a ranar 17 ga Janairu, 2026, inda aka kashe matar da ’ya’yanta cikin wani mummunan yanayi da ya girgiza al’ummar jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Sanarwar ta ce kama waɗanda ake zargin ya biyo bayan umarnin Babban Sufeton ’Yan Sanda na ƙasa, Kayode Egbetokun, inda kwamishinan ’ƴansandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya jagoranci wani kwakkwaran bincike na sirri da ya kai ga nasarar cafke waɗanda ake zargin.

Mutanen da aka kama sun haɗa da Umar Auwalu, mai shekaru 23, ɗan yankin Sabuwar Gandu, Isyaku Yakubu wanda aka fi sani da Chebe, mai shekaru 40 daga Sagagi, da kuma Yakubu Abdulaziz mai laƙabin Wawo, dan shekaru 21 daga Sabon Gida Sharaɗa.

Rundunar ta ce an kama su ne a wani samame na musamman da aka gudanar daga ƙarfe 10 na daren 17 ga Janairu zuwa karfe 4 na safiyar 18 ga Janairun 2026.

A yayin bincike, jagoran ƙungiyar, Umar Auwalu, wanda ɗan uwa ne ga marigayiyar, ya amsa laifin aikata kisan, tare da iƙirarin cewa sun aikata makamantan laifuka a baya, ciki har da kisan wasu mata biyu da aka ƙone a unguwar Tudun Yola a Kano.

Daga hannun waɗanda ake zargin, ’ƴansanda sun kwato tufafi masu ɗauke da jini, wayoyin marigayiyar guda biyu, adda, gora, kuɗin da aka sace a wajen aikata laifin, da kuma wasu makamai masu hatsari.

Rundunar ’ƴansandan ta ce bincike na ci gaba, tare da tabbatar wa al’umma cewa za a gurfanar da dukkanin waɗanda aka samu da hannu da aikata laifin a gaban kotu.

Rundunar ta kuma yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin, tare da godiya ga al’umma bisa addu’o’i, goyon baya da haɗin kai wajen yaƙi da aikata laifuka a Jihar Kano.

Jihar Kano ta fuskanci Kisan gilla guda 8 da aka yi a Kano waɗanda suka tayar da hankalin al’ummar jihar Kano

(1) Ummita da ɗan China

(2) Abdulmalik Tanko da Hanifa

(4) Kisan Ladani a Hotoro

(5) Matar da ta hallaka ƴaƴanta guda 2 saboda mijinta zai kara aure.

(6) Kisan da Hafsa Cucu ta yi wa yaron mai gidanta a Unguwa Uku.

  1. Kone matan Aure biyu a unguwar Tudun Yola
  2. Kisan Mata biyu a unguwar Dorayi bayan gidan Sarki

Tuni dai gwamnan Jihar Kano Injiniya Kabir Abba Yusuf ya miƙa ta’aziyyarsa ga ƴan uwa da iyalan mamatan ya kuma yaba wa runsdunar ƴansanda a kan yadda sukia gaggauta zaƙulo waɗanda suka yi wannan aika-aikar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *