Dakarun soji sun daƙile harin ’yan tawaye kan bututun mai a Nijar

[ad_1]



Dakarun sojin ƙasa sun samu nasarar daƙile wani hari da ’yan tawaye suka kai kan muhimmin bututun ɗanyen mai da ke gabashin ƙasar Nijar.

A cewar rundunar sojin, maharan daga ƙungiyar Patriotic Movement for Freedom and Justice (MPLJ) sun yi yunƙurin kai hari a wani wuri da ke ɗauke da rijiyoyin mai na Agadem a ranar Talata, amma jami’an tsaro sun mayar da martani cikin gaggawa, lamarin da ya tilasta wa ’yan tawayen tserewa tare da barin makamai da kayan aiki.

Bututun mai tsawon kilomita 2,000 na fitar da ɗanyen man Nijar zuwa tashoshin jiragen ruwa na ƙasar Benin, tare da haɗin gwiwar kamfanin China National Petroleum Corporation (CNPC).

Sai dai ƙungiyar MPLJ ta ce ta yi wa sojojin “mummunar asara”, inda ta yi iƙirarin kashe aƙalla sojoji 24 tare da lalata wasu muhimman kayayyakin man fetur.

Ƙungiyar ta kuma gargaɗi kamfanin CNPC kan duk wata hulɗa da gwamnatin mulkin soji ta Janar Abdourahamane Tiani, wadda ta karɓi mulki a watan Yulin 2023.

MPLJ na kira da a dawo da tsohon shugaban ƙasa Mohamed Bazoum da aka hamɓarar tare da zargin cewa al’ummomin yankin arewa maso gabas ba sa cin moriyar arzikin man fetur yadda ya kamata.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *