Ofisoshin Jakadancin Sin A Lagos Na Najeriya Da Senegal Sun Shirya Jerin Harkoki Don Murnar Sabuwar Shekarar Gargajiyar Sinawa
[ad_1]
A ranar 8 ga wata, karamin ofishin jakdancin kasar Sin da ke Lagos, tarayyar Najeriya ya shirya jerin harkoki don murnar sabuwar shekarar gargajiyar Sinawa ta 2026, ciki har da liyafar murnar sabuwar shekarar gagajiyar Sinawa da cika shekaru 55 da kulla huldar diflomasiyya a tsakanin Sin da Najeriya.
Liyafar ta samu halartar Ja’afaru Yakubu, shugaban kwamitin kula da dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Sin na majalisar wakilai ta Najeriya, da Biodun Ogunleye, shugaban hukumar kula da makamashi da ma’adanai ta gwamnatin Lagos, da wakilan Sinawa mazauna wurin, da karamin jakadan kasa da kasa da ke Lagos, da kuma shugabannin hukumomin diflomasiyya na kasa da kasa, wadanda yawansu ya kai kimanin 2200.
Yan Yuqing, karamar jakadiyar Sin da ke Lagos ta yi jawabi a yayin liyafar, inda ta isar da gaisuwar murnar sabuwar shekarar Sinawa ga sassa daban daban na Sin da Najeriya, kana ta waiwayi manyan nasarorin da kasar Sin ta samu ta fuskar tattalin arziki da babban ci gaban da aka samu wajen raya dangantakar da ke tsakanin Sin da Najeriya a cikin shekarar da ta gabata, baya ga bayyana fatan ganin yadda bangarorin biyu za su raya huldarsu yadda ya kamata. A cewarta, Sin na son more damammakin bunkasa tare da Najeriya, Afirka da ma duniya baki daya.
A cikin jawabin da ya yi, Ja’afaru Yakubu ya bayyana cewa, a cikin shekaru 55 da suka gabata bayan kulla huldar diflomasiyya a tsakanin Najeriya da Sin, bangarorin biyu sun hada kansu sosai, inda sakamakon hakan ya amfanar da al’ummunsu. Sin na daya daga cikin muhimman aminan Nijeriya mafiya muhimmanci.
A gun liyafar, an haska fim na tallata shirin talabijin na shagalin murnar sabuwar shekarar gargajiya ta doki ta Sinawa, da babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) zai gabatar, wanda ya samu jinjina wa daga masu kallo.
Ban da wannan kuma, a daren ranar 9 ga wata bisa agogon wurin, ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Senegal ya shirya liyafar murnar sabuwar shekarar gargajiyar Sinawa ta 2026 a Dakar, babban birnin kasar, inda aka ma haska fim na yayata shirin talibijin na shagalin sabuwar shekarar gargajiyar Sinawa na CMG. (Kande Gao)
[ad_2]
Source link