NNPP Ta Rushe Shugabancinta A Kano Biyo Bayan Jita-jitar Sauya Sheƙar Abba Zuwa APC
Jam’iyyar NNPP ta rushe shugabancinta a Jihar Kano, ciki har da shugabbannin ƙananan hukumomi da na mazaɓu.
Wannan mataki na zuwa ne biyo bayan jita-jitar sauya sheƙar Gwamna Abba Yusuf zuwa jami’yyar APC.
- Tinubu Ya Gudanar Da Ayyukan Raya Kasa Da Dama A Arewa A 2025 —Abdul’aziz Abdul’aziz
- Sojoji Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga A Jihar Kano
Oladipo Johnson, Sakataren yaɗa labarai na NNPP na ƙasa, ya ce jam’iyyar za ta kafa kwamitin wucin gadi nan ba da jimawa ba don kula da al’amuran jam’iyyar.
Wannan lamari ya biyo bayan jita-jitar ɓarkewar rikici tsakanin jagoran NNPP na ƙasa kuma tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Ana sa ran gwamnan zai koma jam’iyyar APC, sai dai Kwankwaso da wasu jiga-jigan NNPP na adawa da hakan.
Jam’iyyar APC a Kano ta shirya karɓar Gwamna Abba zuwa cikinta.
Johnson, ya jaddada cewa rushe shugabannin jam’iyyar a Kano, an yi shi ne bisa doka da tsarin jam’iyya.
Ya ce jam’iyyar ta gode wa tsoffin shugabannin bisa gudunmawarsu, kuma za a sanar da yadda za a kafa kwamitin wucin gadi nan gaba.