Iran ta ci gaba da luguden wuta bayan ɗan Khamenei ya karɓi ragamar mulki

[ad_1]



Iran ta harba makamai masu linzami kan Isra’ila da wasu ƙasashen Larabawan Tekun Fasha da safiyar Litinin, bayan da ƙasar ta sanar da Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoranta domin maye gurbin mahaifinsa, Ayatollah Ali Khamenei da aka kashe a hare-haren Amurka da Isra’ila.

Hare-haren sun zo ne kwanaki tara bayan farmakin haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila ya kashe Ali Khamenei, lamarin da har yanzu ke ci gaba da rura wutar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.

Majalisar ƙoli ta malamai ta Iran mai mambobi 88 ce ta zaɓi Mojtaba Khamenei mai shekara 56 a matsayin jagora na uku tun bayan juyin juya halin Musulunci na 1979, kamar yadda aka sanar a gidan talabijin na gwamnatin Iran.

Sanarwar ta ce majalisar ba ta yi jinkiri ba wajen zaɓen sabon jagora duk da abin da ta kira “ta’addancin Amurka da gwamnatin sahayoniyawa”.

A yayin da Iran ke kai hare-hare, Isra’ila ma ta ƙaddamar da sabbin farmakai kan muhimman cibiyoyi a tsakiyar Iran, yayin da yaƙin ke ƙara faɗaɗa a yankin.

Ƙasashen Saudiyya, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Kuwait sun ce sun fuskanci hare-haren makamai masu linzami ko jiragen marasa matuƙa, yayin da Bahrain ta ce an kunna ƙararrawar gaggawa bayan hare-hare.

Farashin gangar man fetur ya zarce dala 100

Yaƙin ya kuma girgiza kasuwannin duniya, inda farashin ɗanyen mai ya haura dala 100 kan kowace ganga a karon farko tun bayan yaƙin Rasha da Ukraine shekaru huɗu da suka gabata.

Dangane da yadda farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabo a kasuwar duniya a dalilin yaƙin, Trump ya ce tashin farashin na wani ɗan lokaci ne, kuma gara ɗaukar wannan ƙaddarar a kan barin Iran ta mallaki makamin Nukiliya.

Mun fafata da sojojin Isra’ila — Hezbollah

A wani ɓangaren kuma, mayaƙan Hezbollah masu samun goyon bayan Iran sun ce sun fafata da sojojin Isra’ila da suka sauka a gabashin Lebanon ta jirage masu saukar ungulu 15 daga kan iyakar Syria.

Ma’aikatar Lafiyar Lebanon ta ce aƙalla mutum 394 ne suka mutu tun bayan fara yaƙin, ciki har da yara 83 da mata 42.

Hare-haren Iran sun kuma jikkata mutum 32 a Bahrain, yayin da Saudiyya ta ce mutum biyu sun mutu bayan wani makami ya faɗa a lardin Al-Kharj.

A Isra’ila kuwa, mahukunta sun ce hare-haren makamai masu linzami na Iran sun kashe mutum 10, yayin da sojoji biyu suka mutu a Lebanon.

Ma’aikatar Lafiyar Iran ta ce sama da fararen hula 1,200 sun mutu tare da jikkata kusan 10,000, sai dai AFP ta ce ba ta iya tabbatar da waɗannan alƙaluma da kanta ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *