[ad_1]
Gwamnan Jihar Adamawa, Umaru Fintiri, ya kaddamar da rabon tallafin gaggawa na sama da Naira Biliyan 1 ga mutane sama da 5,000 da ambaliyar ruwa ta shafa a shekarar 2025 a Karamar Hukumar Yola ta Kudu ta Jihar.
Fintiri ya ce gidaje da ambaliyar ruwa ta shafa kaɗan za su sami Naira 135,000, matsakaita za su sami Naira 280,000, sai kuma waɗanda na su yafi ƙamari, za su sami Naira 550,000 kowannensu.
- Lambobin NIN Da CAC Za Su Zama Lambobin Biyan Haraji Daga 2026— FIRS
- Ɓangaren Ilimi Ya Samu Rinjaye A Kasafin ₦985.9bn Na 2026 Da Gwamna Sani Ya Sanya Wa Hannu
Bikin kaddamar da tallafin, wanda aka gudanar a Kwalejin Aliyu Mustapha da ke Yola, manyan jami’an gwamnati, masu ruwa da tsaki, da kuma al’ummomin da abin ya shafa, duk sun samu halarta.
Fintiri ya bayyana cewa, an rarraba waɗanda abin ya shafa zuwa kashi uku bisa la’akari da irin ɓarnar da ambaliyar ta yi.
Gwamnan ya kuma shawarci mutanen da ke zaune a yankunan da ambaliyar ruwa ke yawan shafa da su koma wurare mafi aminci, yana mai tabbatar musu da goyon bayan gwamnati wurin tallafa musu.
[ad_2]
Source link