Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Zurfafa Kwazo Wajen Aiwatar Da Shirin Raya Kasa Na Shekaru 5 Karo Na 15
[ad_1]
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya yi kira da a kara zurfafa kwazo wajen fayyace matakan aiwatar da shirin raya kasa na shekaru 5 karo na 15 da aka ayyana, domin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar Sin.
Li Qiang, wanda memba ne a ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya yi kiran ne a jiya Litinin, yayin da yake jagorantar taron majalisar gudanarwar kasar Sin dangane da tsara matakan aiwatar da shirin.
Ya ce tuni an riga an samar da ginshikan tsara matakan gudanarwa, kuma mataki na gaba shi ne a kara kaimin tacewa da bunkasa tsara matakan cikin matukar tsanaki.
Li, ya jaddada muhimmancin bunkasa sabon karfin samar da hajoji, da bude sabbin babukan bunkasa kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da gaggauta samar da sabbin ginshikan ci gaba, da kyautata, da daukaka tsarin raya tattalin arzikin kasar Sin.
Bugu da kari, firaministan na Sin ya yi kira da a yi aiki tukuru don biyan bukatun al’umma, da kaddamar da jerin manufofi, da ayyuka da za su amfani jama’a, da zakulo sabbin matakan ingiza ci gaban tattalin arziki tare da kyautata rayuwar jama’ar kasa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link