EFCC Ta Cafke Mutane 20 A Zaɓen FCT, Ta Kwato Sama Da Miliyan 17 Wajen Masu Sayen Ƙuri’a
[ad_1]
Jami’an EFCC sun cafke mutane 20 bisa zargin aikata laifukan zaɓe a zaɓen ƙananan hukumomin Babban Birnin Tarayya (FCT) da aka kammala. Hukumar ta ce ta kuma kwato sama da Naira miliyan 17 da ake zargin an tanada domin sayen ƙuri’u.
A sanarwar da ta wallafa a shafinta na X, EFCC ta ce an kama waɗanda ake zargin ne a ranar 21 ga Fabrairu, 2026, a yankunan Abaji (2), da Gwagwalada (9), da Kuje (4) da Kwali (4). Laifukan da ake zarginsu sun haɗa da saye da sayar da ƙuri’a da kuma hana jami’ai gudanar da aikinsu.
- DSS Ta Kama El-Rufai Bayan EFCC Ta Bayar Da Belinsa
- Wani Direba Da Ya Buge Mai PoS Har Lahira Ya Tsere A Abuja
Hukumar ta ce an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin da Naira miliyan 13.5 a cikin wata mota da aka ajiye kusa da rumfar zaɓe a ƙaramar hukumar Kwali. Jimillar kuɗin da aka kwato ya kai N17,218,700.
Zaɓen na 21 ga Fabrairu ya gudana a dukkanin ƙananan hukumomi shida na FCT da suka haɗa da: Abaji, da Bwari, da Gwagwalada, da Kuje, da Kwali da Abuja Municipal Area Council (AMAC). Masu sa ido kan zaɓe, ciki har da Centre for Democracy and Development, sun ruwaito bayar da kuɗi tsakanin N1,000 zuwa N5,000 ga masu zaɓe a wasu rumfuna, musamman a Gwagwalada da Kuje.
Sakamakon da INEC ta sanar ya nuna cewa APC ta lashe kujerun shugabancin ƙananan hukumomi biyar, yayin da PDP ta samu kujera ɗaya. EFCC ta ce za ta gurfanar da waɗanda ake zargi a kotu bayan kammala bincike.
[ad_2]
Source link