Sarkin Musulmi Ya Taya Ladoja Murnar Zama Sabon Sarkin Ƙasar Ibadan
Sarkin Musulmi kuma shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Nijeriya (NTRCN), Mai Martaba Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya mika sakon taya murna ga Oba Alhaji Rashidi Adewolu Ladoja, saboda nadinsa a matsayin sabon Olubadan kuma sarki na 44 a kasar Ibadan. Sarkin, a cikin wani sako da ya fitar a safiyar ranar Alhamis mai dauke…