An tsinci gawar saurayi a gefen kudiddifi a Kalaba
An tsinci gawar wani saurayi mai suna Daniel Ekanen, mai kimanin shekaru 18, a gefen wani kudiddifi da ke unguwar Ikot Effanga a Ƙaramar Hukumar Kalaba, Jihar Kuros Riba. Lamarin ya jefa firgici a zukata da kuma zaman dar-dar a cikin mazauna yankin, inda aka ruwaito cewa an kawo marigayin ne wurin…