Category: Latest News

  • Ƙungiyoyin Farar Hula Sun Nemi A Dakatar Da Jami’an Gwamnatin Kao

    [ad_1]

    Ƙungiyoyin farar hula (CSOs) a Kano sun buƙaci a gaggauta dakatarwa da gurfanar da jami’an gwamnati da aka zarga da hannu a badaƙalar rashawa da ta kai biliyoyin Naira. Wannan kiran ya biyo bayan rahotannin da suka nuna cewa Daraktan sashin huldar fadar Gwamnati, Abdullahi Ibrahim Rogo, ya karkatar da Naira biliyan 6.5 tsakanin Nuwamba 2023 da Fabrairu 2025 ta hannun kamfanoni daban-daban ta hanyar kwangilolin bogi.

    Haka kuma, hukumar ICPC ta kammala bincike a wata badaƙalar Naira biliyan 1.02 da ya shafi Shugaban hukumar Zaɓe ta jihar Kano (KANSIEC), Farfesa Sani Lawan Malumfashi, Sakataren hukumar Anas Mustapha, da Darakta Ado Garba, inda suka fitar da kuɗi daga asusun hukumar zuwa kamfani mai zaman kansa duk da cewa an biya ma’aikatan wucin gadi ta hanyar bankuna.

    A cikin wata sanarwa da ƙungiyoyi 20 suka sanya hannu, sun bayyana wannan zargi a matsayin babbar alama ta cin hanci da rashawa da ke barazana ga tafiya da mulki, da tattalin arziƙi, da kuma amincewar jama’a da gwamnati. Sun ce irin wannan ɓarna tana rage zuwan masu zuba jari da karya ƙwarin gwuiwar matasa kan amana da cancanta.

    Ƙungiyoyin sun buƙaci a gurfanar da duk wadanda aka zarga, a gudanar da bincike na musamman kan dukkan ma’aikatu da hukumomin jiha, a ƙarfafa rawar majalisar dokoki wajen sa ido, da kuma samar da kariya ga masu fallasa gaskiya. Haka zalika, sun buƙaci kafa dandalin tattaunawa da NGOs da shugabannin al’umma don ƙarfafa mulkin da zai mayar da hankali ga jama’a.

    A cewarsu: “Jihar Kano na tsaye a kan tsauni. Ko dai mu fuskanci cin hanci kai tsaye mu dawo da amana a shugabanci, ko kuma mu bari mu faɗo  cibiyoyinmu da makomar ‘ya’yanmu ta tuguje,” in ji sanarwar.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Makomar Najeriya na hannun matasa —Malaman addini

    [ad_1]



    Malaman addinin Musulunci da shugabannin al’umma sun buƙaci matasan Najeriya da su rungumi rayuwa mai ma’ana bisa koyarwar addini, suna gargaɗi cewa watsi da tarbiyyarsu na iya jefa makomar ƙasa cikin haɗari.

    An yi wannan kira ne a taron ’Light of Guidance Youth Conference 2025’ da aka gudanar a Abuja, wanda ƙungiyoyin Light of Guidance Foundation da Ma’aruf Foundation suka shirya.

    Uwargidan Gwamnan Jihar Yobe, Hajiya Hafsat Kollere-Buni, ta shaida wa mahalarta taron cewa matasa su ne “kadarar ƙasa mafi daraja,” don haka dole a jagorance su da koyarwar Musulunci domin su jagoranci al’ummarsu cikin mutunci.

    “Idan muka jagorance su bisa koyarwar Musulunci, za su kai al’ummarmu gaba cikin martaba da mutunci. Amma idan muka yi watsi da su, muna iya rasa makomarsu da ma tamu baki daya,” in ji ta.

    Daraktan Gudanarwa na Gidauniyar Light of Guidance, Mohammad Khamis Ahmad, ya ce an shirya taron ne domin magance rashin tsari da manufar rayuwa da ya karaɗe matasa.

    Sauran masu jawabi sun haɗa da Shugaban Islamic Media Nigeria, Aliyu Rashid Makarifi, wanda ya ce matasan yau su ne shugabannin gobe, a yayin da da Farfesa a fannin Tattalin Arziki a Jami’ar Nile, Ahmed Adamu, ya gargaɗi game da tasirin kafofin sada zumunta da son kayan duniya.

    Taron ya kunshi laccoci, tattaunawa da domin ƙarfafa tarbiyyar addini da na halin kirki a tsakanin matasa.


    [ad_2]

    Source link

  • Tinubu Ya Isa Brazil, Zai Nemi Masu Zuba Jarin Biliyoyi A Noma, Makamashi Da Fasaha

    [ad_1]

    Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Brasilia, babban birnin ƙasar Brazil, domin ziyarar aiki ta kwanaki biyu a kan gayyatar takwaransa, Shugaba Luiz Inácio Lula da Silva.

    Wannan ziyara na nuni da sabon yunƙurin ƙarfafa dangantakar tattalin arziƙi da siyasa tsakanin Nijeriya da ƙasar Brazil, wacce ita ce mafi girma a Latin Amurka. Ana sa ran wannan tafiya za ta haifar da jarin biliyoyin daloli musamman a ɓangaren noma, da makamashi, da fasahar zamani.

    A lokacin ziyarar, Shugaba Tinubu zai gudanar da tattaunawa ta musamman da Lula da Silva, sannan kuma zai halarci Taron Kasuwanci tsakanin Nijeriya da Brazil, inda zai gana da manyan masu zuba jari. Haka kuma, za a sanya hannu kan muhimman yarjejeniyoyi da takardun fahimtar juna (MoUs).

    A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, babban abin da aka fi mayar da hankali a kai shi ne aiwatar da jari a fannin noma da aka daɗe ana tattaunawa a kai, ciki har da ci gaba da aikin $1.1 biliyan Green Commuse Project, da kuma jawo sabbin jarin ƙasashen waje a ɓangaren noma da makamashi.

    Haka kuma, jami’an gwamnati sun bayyana cewa wannan ziyara za ta ƙara haɗin gwuiwa a fannin sufurin jiragen sama, da sabunta makamashin, da musayar al’adu, da sauyin fasahar dijital.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

    [ad_1]

    Jami’an rundunar ƴansanda ta jihar Nasarawa sun samu nasarar cafke wani shahararren shugaban ƴan fashi da masu garkuwa da mutane, Mohammed Bammi wanda aka fi sani da Zomo, tare da wasu abokan aikinsa a yayin wani babban sumamen da suka kai kan miyagu a jihar.

    Rundunar ta bayyana cewa Zomo ya daɗe yana jagorantar garkuwa da mutane da fashi a yankin ƙaramar hukumar Doma da kewaye. An cafke shi ne yayin wani sumamen tsaftace dajin Doka da jami’an sashin Doma suka gudanar, bayan ya tsere a watan Yuli. An ce ya yi yunƙurin kai wa jami’an hari da wuka lokacin da za a damƙe shi, amma aka rutsa shi aka kama shi da ransa.

    Kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Ramhan Nansel, ya ce bincike ya kai jami’an zuwa maɓoyar Zomo a ƙauyen Alagye, Doma, inda suka gano makaman da suka haɗa da bindigar Pump Action, da bindigar AK-47 da aka haɗa ta a gida tare da mazaganya, da harsasai guda biyu da alburusai guda biyar, da wuka, da igiya, da wayoyi biyu, da kuma kayan sanya wa na jami’an NSCDC.

    Haka kuma, Nansel ya ce jami’an rundunar Awe sun cafke wasu mutane biyar da ke cikin wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane 10 bayan samun sahihan bayanai. An kama su ne a ƙauyen Gidan Taku. Waɗanda aka cafke sun haɗa da Michael Ato, da Richard Ato, da Alom Bernard, da Hangior Ato da Jacob Hunde (wanda aka fi sani da Okocha). An kwace bindigogi biyu na AK-47 da aka yi a gida da harsashi guda daya daga hannunsu.

    Kakakin ya ƙara da cewa bincike ya gano cewa a watan Afrilu 2024 wannan ƙungiya ta taɓa sace mijin Blessing John, mai suna John Ada Kuje, inda suka karɓi kuɗin fansa kafin su sake shi. Kwamishinan ƴansanda na jihar, CP Shetima Jauro Mohammed, ya jinjinawa jami’an bisa kwazo da sadaukarwa tare da jan hankalinsu da su ci gaba da matsa lamba har sai an kawar da masu garkuwa da mutane da ƴan fashi a jihar. Duk waɗanda aka kama an mika su ga sashi na musamman na masu garkuwa da mutane domin ƙarin bincike da gurfanarwa a kotu.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Za A Bude Cibiyar Watsa Labarai Game Da Bukukuwan Nasarar Yaki Da Harin Japan

    [ad_1]

    A ranar 27 ga watan nan na Agusta, za a bude cibiyar tattarawa da watsa labarai game da bukukuwan cika shekaru 80 da samun nasara a yakin turje wa harin Japan da karshen yakin duniya na II.

    Cibiyar wadda take hotel na Beijing Media Center, za ta bayar da shaidar watsa labarai da shirya damarmakin hirararki ga ‘yan jarida na kasar Sin da na ketare. (Fa’iza Mustapha)




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Yadda matasa suka yi aikin gayya don gyara hanyoyi a Kafanchan

    [ad_1]



    Matasa da dama a garin Kafanchan, da ke Ƙaramar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, sun yi aikin gayya domin gyara hanyar garin.

    Sun yi amfani da gatari, fatanya, diga da sauran kayan aiki wajen yi wa hanyar gyara.

    Aikin ya haɗa da haƙa da faɗaɗa magudanan ruwa don kaucewa ambaliya da kuma hana hanyar ƙara lalacewa.

    Shugaban ƙungiyar Kafanchan Youth Forum, Injiniya Sa’adu Bako, ya ce sun yi aikin ne domin rage wahalar da jama’a ke sha, musamman wajen zuwa jana’iza, musamman a lokacin damina.

    Ya kuma yi kira ga gwamnati ta gyara hanyar, kasancewar ba maƙabarta kaɗai take kai wa ba, har da ƙauyukan manoma kamar Zauru da Kurdan.

    “Ina kira ga Gwamna Uba Sani ya saurari koke-kokenmu, domin gyaran hanyar don sauƙaƙa rayuwar jama’a kuma ya taimaka wajen harkar kasuwanci da fitar da amfanin gona,” in ji shi.

    Ya gode wa matasan da suka fito aikin sa-kan da kuma mutanen da suka tallafa musu da kuɗi da kayan aiki.

    Wasu mazauna yankin sun kuma roƙi gwamnati ta kula da hanyoyin cikin garin Kafanchan, kasancewar jama’ar yankin manoma ne da ke buƙatar hanyoyin mota don fitar da amfanin gonakinsu.

    Go hotunan yadda matasan suka gudanar da aikin:


    [ad_2]

    Source link

  • An Kaddamar Da Makon Fina-finai Da Shirye-shiryen Talabijin Na SCO A Qingdao

    [ad_1]

    An kaddamar da makon nuna fina-finai da shirye-shiryen talabijin na kungiyar hadin kai ta Shanghai (SCO), ranar Juma’a a Qingdao mai taken “Duniya ta hadu ta hanyar haske da inuwa a Qingdao”, lamarin da ya mayar da birnin zuwa cibiyar musayar al’adu da bukukuwan nuna fina-finai.

    Shirin wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG da gwamnatin birnin Qingdao suka shirya, da taimakon hukumar kula da shirya fina-finai ta Sin, zai gudana tsawon mako guda, inda ya hada mashirya fina-finai da jagororin masana’antar da jami’ai kamar sakatare janar na SCO da shugabannin CMG da manyan jami’an diplomasiyya da masu wakiltar al’adu da taurarin fina-finai da masu tsara shirye-shirye a shafukan sada zumunta da ‘yan kallo daga kasashe mambobin kungiyar SCO, domin zurfafa musayar al’adu da lalubo damarmakin hadin gwiwa a masana’antar shirya fina-finai. (Fa’iza Mustapha)




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Ɗaliba ta haɗu da ajalinta a hatsarin mota a Yobe

    [ad_1]



    Amina Yakubu, ɗaliba a ajin farko a Sashen Ilimin Halittu na Jami’ar Jihar Yobe (YSU), ta rasu a wani hatsari da ya rutsa da ita a Damaturu.

    Sanarwa daga ofishin mataimakin shugaban jami’ar da Abdulmumin Kolo Gulani, ta fitar ta tabbatar da rasuwar ɗlaibar.

    Ɗalibai da malaman jami’ar sun bayyana jimaminsu game da rasuwarta.

    Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin ranar Asabar a kan titin Gujba daura da ƙofar jami’ar.

    Keke Napep da ɗalibar ke ciki ne ya yi taho mu gama da wata mota wadda ta murƙushe su.

    A cewar sanarwar, wasu mutum huɗu sun samu raunuka.


    [ad_2]

    Source link

  • CMG Za Ta Gabatar Da Bikin Faretin Soja Na Beijing Cikin Harsuna 85 Ga Duk Fadin Duniya

    [ad_1]

    Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, za ta yi amfani da harsuna guda 85, don gabatar wa duk fadin duniya bikin cika shekaru 80 da al’ummar Sinawa suka yi nasara a yakin turje wa kutsen Japanawa da karshen yakin duniya na II, gami da gagarumin bikin faretin soja a Beijing.

    Domin gabatar da rahotanni da shirye-shirye masu inganci game da bikin zuwa ga duk fadin duniya, CMG ta fara amfani da karin wasu sabbin harsuna guda uku wajen watsa shirye-shiryenta a kwanakin baya, ciki har da Irish, da Tok pisin, da kuma harshen Rwanda. Daga cikinsu, yawan masu amfani da harshen Rwanda ya zarce miliyan 13, wadanda ke zaune a kasashen Rwanda, Burundi, Uganda da kuma Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.

    Amfani da karin harsunan uku, zai fadada yankunan da ke iya karbar shirye-shirye da CMG ke gabatarwa a yammacin Turai, da kudancin yankin tekun Pasifik gami da tsakiya da gabashin Afirka, al’amarin da ya sa CMG ta ci gaba da zama babbar kafar watsa labarai dake amfani da harsuna mafi yawa a duniya wajen watsa shirye-shirye. (Murtala Zhang)




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • An Kaddamar Da Gini Mara Fitar Da Hayakin Carbon Irinsa Na Farko A Duniya

    [ad_1]

    A yau Lahadi, aka kaddamar da wani sabon gini irinsa na farko na zamani, da ba ya fitar da hayakin carbon ko kadan, a birnin Qingdao na lardin Shandong dake gabashin kasar Sin. Wannan wata gagarumar nasarar ce a kokarin kasar na kawar da fitar da hayakin carbon baki daya.

    Yayin da ake bukatar kilowatta sa’a 6,000 a kowacce rana, ginin ofishin mai tsawon mita 117 na dauke da kayayyaki na fasahohin zamani masu inganci da suka maye gurbin masu gurbata muhalli da makamshi mai tsafta 100 bisa 100.

    Ba kamar sauran gine-ginen da aka saba gani da ake shimfida musu allunan sola a sama ba, a wannan gini akwai bangon gilas dake samar da lantarki daga hasken rana a bangarorin gabas da kudu da yammacinsa.

    Wannan yana samar da lantarki da rage asarar makamashi da kuma samar da kaso 25 na bukatun makamshi na ginin. Haka kuma zai kai ga rage fitar hayakin Carbon tan 500 a shekara.

    Baya ga haka, ginin na amfani da tsoffin baturan motoci masu amfani da lantarki, wajen adana makamashi. Ana amfani da irin wadannan batura guda 14 wajen adana rarar makamashin da ake samu daga bangon gilas mai zukar hasken rana da samar da makamashi mai tsafta a lokaci mafi samun hasken rana, a farashin yuan 0.22 kwatankwacin $0.031, kan kilowatt 1 a kowacce sa’a. Kuma za a yi amfani da makamashin da aka adana a lokacin da ake bukatar lantarki mai yawa ko kuma lokacin da ake da karancin hasken rana domin daidaita bukatar makashi. (Fa’iza Mustapha)




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link