Category: Latest News

  • Gwamnatin Sokoto Ta Ƙaryata Rahoton NBS Kan Talauci, Ta Ƙaddamar Da Sabon Bincike

    [ad_1]

    Gwamnatin Jihar Sokoto ta ƙaryata rahoton Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) da ya nuna cewa jihar ce ke da mafi yawan tsananin talauci a Nijeriya, inda ta bayyana cewa hanyar da aka yi amfani da ita wajen binciken bata wadatar ba.

    Kwamishinan tsare-tsare da bunƙasar tattalin arziƙi na jihar, Dr. Abubakar Muhammad Zayyanu, ya bayyana haka yayin taron manema labarai a wani taron bita na yini guda da aka shirya tare da haɗin gwuiwar Uncefda tarayyar turai da sauran abokan cigaba a Sokoto. Ya ce binciken na NBS da aka gudanar tun a 2022 bai nuna halin da ake ciki a yanzu ba.

    Dr. Zayyanu ya bayyana cewa gwamnatin jihar tare da kamfanin Red Wire sun gudanar da sabon bincike domin tantance matsayin talauci daga lokacin binciken NBS zuwa yanzu. Ya ce gwamna ya amince da sabon binciken domin tabbatar da sahihancin bayanai, kuma rahotannin farko sun nuna an samu wasu cigaba masu kyau.

    Ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta wallafa cikakken sakamakon binciken bayan kammala nazarin bayanan. Haka kuma ya tuna cewa a taron Majalisar zartarwa ta ƙasa (NEC) da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta, an gabatar da shirin Bankin Duniya da zai duba tattalin arziƙi da yawan jama’a daga matakin gunduma.

    Zayyanu ya ce gwamnatin Sokoto tana amfani da tsarin “bottom-up approach” wajen tattara bayanai daga ƙananan hukumomi da mazabu 886, domin samar da ingantattun hanyoyin magance talauci ta hanyar bayanai da aka tabbatar da sahihancinsu.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Harin Asibitin Gaza Ya Halaka Mutane Da Dama, Ciki Har Da Ƴan Jarida

    [ad_1]

    Rahotanni daga Gaza sun tabbatar da cewa an kashe ƴan jarida huɗu a wani mummunan hari da aka kai kan asibitin Nasser, ciki har da Mohammed Salama na Al Jazeera, Hossam al-Masri na Reuters, Moaz Abu Taha na NBC, da kuma Mariam Abu Daqa na Associated Press. Wannan ya ɗaga adadin ƴan jaridar da aka kashe tun bayan fara rikicin zuwa a ƙalla 244.

    Hare-haren, wanda Isra’ila ta bayyana a matsayin “sumamen ƙarshe” don mamaye dukkan yankin Gaza, ya ƙara tsananta halin da ake ciki a lokacin da yunwa ta yi ƙamari a yankin. Likitoci sun bayyana cewa babu isassun kayan agaji ko abinci don ceto rayukan yaran da ke fama da tsananin yunwa.

    Shaidu sun bayyana cewa jirgin sama marar matuƙi ne ya fara luguden wuta kan ginin asibitin a safiyar yau, lamarin da ya haifar da girgiza mai tsanani a cikin yankin.

    A cewar rahotanni, mutane 14 ne suka rasa rayukansu nan take a harin, ciki har da ƴan jarida huɗu, wani jami’in agaji, da kuma fararen hula goma, lamarin da ya ƙara dagula rayuwar al’ummar Gaza da ke ci gaba da fuskantar hare-hare da tsanantawar yunwa.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Jiragen yaki sun kashe ’yan ta’adda 35 a iyakar Najeriya da Kamaru

    [ad_1]



    Sojojin Najeriya sun kashe ’yan ta’adda kimanin 35 da ake zargin mayakan kungiyar ISWAP ne a kusa da iyakar Najeriya da Kamaru.

    ’Yan ta’addan sun taru a yankin Kumshe, wani gari da ke kan iyaka a Jihar Borno, da safiyar Asabar domin kai hari kan sansanin sojoji da ke yankin.

    Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa bayan samun bayanan sirri, sojojin kasa sun nemi taimakon rundunar sojin sama, inda jiragen yaki suka kai hare-hare a wuraren da aka gano ’yan ta’addan sun taru.

    “Ranar Asabar, 23 ga Agusta, sojojin runduna ta 21 sun dakile wani hari da ’yan ta’adda suka kai da daddare, inda jiragen yaki suka ragargaza ’yan ta’addan,” in ji wata majiya.

    Binciken bayan harin ya nuna cewa an binne gawarwaki fiye da 20, ciki har da sassan jikin da suka tarwatse, an kuma kwato makamai daga hannun ’yan ta’addan.

    Kakakin rundunar sojin sama, Iya Komodo Ehimen Ejodame, ya tabbatar da harin, yana mai cewa fiye da ’yan ta’adda 35 ne aka kashe a hare-haren.

    Ya ce rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen murkushe ’yan ta’adda a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.


    [ad_2]

    Source link

  • Jami’an tsaro sun tsare jagoran Falasdinawa mazauna Najeriya

    [ad_1]



    Jami’an tsaron Najeriya sun yi awon gaba da Shugaban al’ummar Falasdinawa mazauna Najeriya, Abu Ramzi Ibrahim, a birnin Abuja

    Rahotanni sun suna jami’an tsaro sun kama Abu Ramzi Ibrahim me a gidansa da ke Abuja tun ranar Juma’a.

    Majiyoyi daga cikin al’ummar Falasɗinu sun ce Ibrahim, wanda dasn Bafalasɗine ne kuma ya yi karatu a jami’ar Najeriya, yana tsare har zuwa yanzu.

    Wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin Jakadan Falasɗinu da ke Najeriya amma hakarsa ta cin ma ruwa ba.

    Ibrahim ya shahara wajen kare muradun Falasɗinawa ta kafafen yaɗa labarai, musamman a ’yan watannin nan da rikicin Isra’ila da Falasɗinu ke ƙara ɗaukar hankalin duniya.

    Har zuwa yanzu babu wata sanarwa daga hukumomin tsaro kan batun kama shi.


    [ad_2]

    Source link

  • ’Yan Arewa sun bukaci a biya su diyya

    [ad_1]



    ’Yan Arewa a Kasuwar Alaba Rago, shahararriyar kasuwar ’yan Arewa a Jihar Legas sun roki gwamnatin jihar ta biya su diyya kan asarar da suka yi sakamakon rushe kasuwar da gwamnati nta yi.

    Sun bayyana cewa asarar da suka tafka ta haura Naira biliyan 20 bayan Gwamnatin Legas ta rusa masallatai sama da 40 da shaguna kimanin 3,000 a Kasuwar wadda suka kafa shekara 45 da suka gabata a jihar.

    A karo na biyu a ’yan kwanakin nan mahukunta a Jihar Legas suka rushe sassa da dama na kasuwar, wadda ta yi fice da kasuwancin kayan abinci da dabbobi da karafa da sauran kayan masarufi, wacce Hausawa suka kafa a shekarar 1979.

    A cikin watan Mayun 2024, jami’an hukumar ’yan sandan jihar Legas sun mamaye kasuwar, inda suka ce an gudanar da aikin ne domin kawar da bara-gurbi a kasuwar.

    A ranar Lahadin makon jiya, 17 ga watan Agusta, kuma aka fara rusau na baya-bayan nan a kasuwar, lamarin da ya ci gaba zuwa ranar Laraba 20 ga watan Agustan, inda dubban ’yan kasuwa suka rasa matsugunnansu.

    Alhaji Adamu Katagum, Wazirin Sarkin Alaba Rago, ya shaida wa Aminiya cewa sama da shaguna 3,000 ne aka rushe ciki har da masallatai 40, inda ya kiyasta cewa asarar da ’yan kasuwa suka yi ya haura Naira biliyan 20.

    Ya ce ’yan Arewa ne suka kafa kasuwar tun lokacin da wajen yake jeji ne da kuzazzabai, inda suka zuba jari mai yawa don bunkasa ta.

    “A wancan lokacin, wannan wurin ya kasance da kurmi da fadama, babu hanyar sadarwa, ‘yan kasuwa Hausawa ne suka bunkasa ta da albarkatunsu da kuma kudin shigarsu tsawon shekaru da dama.

    “Gwamnati ba ta taba kashe ko sisi daya a nan ba, duk da haka muna biyan haraji da hakkin gwamnati a kowane mataki, sai suka zo suka rushe abin da muka yi ta yi tsawon shekaru 50 muna ginawa ba tare da bin ka’ida ba, wannan babbar asara ce ga mu ’yan Arewa da ke kokarin samun abin dogaro da kai a nan,” Inji Katagum.

    Ya kuma bayyana takaicinsa, inda ya ce, “Mun shafe sama da shekara 50 muna gina wannan kasuwa, mun sha wahala wajen kafa sana’o’inmu a nan, kuma a rana guda suka rusa komai ba tare da gargadi ba, mun kirga akalla masallatai 40 da aka lalata.”

    Muhammed Rabiu ‘Yan Masara

    Wani da abin ya shafa, Alhaji Muhammed Rabiu ’Yan Masara, ya koka da abin da ya bayyana a matsayin rashin adalci duk da irin gudunmawar da ’yan kasuwar ke bayarwa wajen bunkasa tattalin arzikin Jihar Legas.

    Ya kara da cewa al’ummar yankin sun goyi bayan jam’iyya mai mulki a Legas tun a shekarar 1999, kuma ya ce wannan ba hanya ce da ta dace ba don saka musu da biyayyar da suke yi.

    “Mu ’yan Najeriya ne, kuma Legas wani bangare ne na Najeriya, muna da ’yancin kasancewa a nan, inda muka zauna muna fatauci tunda ba komai ba ne sai fadama. Mu ba zaune muke a matsugunan da ba bisa ka’ida ba ne, kadarorinmu suna da takardun doka, kuma muna biyan duk haraji da ake bukata.

    “Duk da haka, mun tashi ne a safiyar ranar Litinin, sai muka yi taho-mu-gama da ’yan sanda dauke da makamai, wadanda suka yi rakiya ga wadanda suka rusa mana dukiyoyinmu da rayuwarmu suka ruguje su cikin kiftawa da bisimillah,” inji Rabiu a cikin wata murya mai cike da damuwa.

    Kawo yanzu dai ’yan kasuwar na ci gaba da kasuwanci a yashe cikin rana da dari yayin da ruwan sama ke bugun su a lokacin da ya sauka.

    Zuwa lokacin hada wannanl labairn yanzu Gwamnatin Jihar Legas ba ta fitar da wata sanarwa ba game da aikin na rusau da aka yi a daya daga cikin kasuwannin jihar da ke tara jama’ar Arewa, kuma kasuwa mafi yawan jama’ar Arewa jihar.


    [ad_2]

    Source link

  • Sojoji Sun Kama Mutane 69 Masu Fasa Bututun Mai A Yankin Neja-Delta

    [ad_1]

    Dakarun rundunar Sojijin Nijeriya sun cafke mutune 69 da ake zargi da hannu a fasa-kaurin mai tare da kwace sama da lita 32,000 na danyen kayayyakin man fetur da aka sace a yayin wani sumame da aka gudanar a sassa daban-daban na Neja-Delta.

    A cikin sanarwar da Lt. Colonel Danjuma Jonah Danjuma, mataimakin daraktan hulɗa da jama’a na 6 Division ya fitar a Fatakwal ranar Lahadi, ya ce aikin ya gudana ne tsakanin 11 zuwa 24 ga Agusta, 2025, tare da haɗin gwuiwar sauran jami’an tsaro, inda aka lalata gudanarwar haramtattun wuraren tace mai tara (9).

    A jihar Delta, an cafke manyan motoci guda biyu dauke da sama da lita 15,000 na man da aka tace ba bisa ka’ida ba a karamar hukumar Sapele, inda aka kama mutum uku da ake zargi da hannu. Haka kuma, a Warri North LGA an gano jarka da ganguna cike da danyen mai da aka tace ba bisa ka’ida ba. A Rivers kuwa, sojoji sun lalata haramtattun wuraren tace mai guda uku, tare da kwace sama da lita 7,000 da kuma kwace jirgin katako guda biyu a Degema da Omoku.

    Haka kuma, a Oyigbo da Okrika an gano sama da lita 3,000 na danyen mai a wuraren da aka kafa wajen tacewa, inda aka kwace ganga, tukunyar dumama da wasu kayan aiki, tare da kama mutum uku da ake zargi. A Bayelsa kuwa, an gano wurin tace mai ba bisa ka’ida ba a Biseni, Yenagoa LGA, inda aka gano tankoki biyu dauke da fiye da lita 7,000 na man da aka sace. A jihar Akwa Ibom kuwa, dakarun soji sun kafa gagarumar sintiri, wanda hakan ya hana masu laifi damar gudanar da ayyukan su.

    Sanarwar ta ce duk mutanen da aka kama an mika su ga hukumomin tsaro domin gurfanar da su a kotu, yayin da kayayyakin da aka kwace aka sarrafa su bisa tsarin aikin

    dakarun.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyan ‘Ya’yan Su

    [ad_1]

    Karin fannoni



    Duk wanda ya shekara arbain zuwa sama ya san irin tarbiyyan da ya samo daga wurin iyayen sa a da baya can, irin mu’amalan dake tsakanin sa da iyaye har ma da shakuwan dake tsakanin ‘ya’ya da iyaye.

    A yanzu kuwa abubuwa sun canza daga yadda aka san su, inda abubuwa suka rincabe sukayi wa iyaye yawa.

    Daya daga cikin manyan sauyin da aka samu sun hada da aikin gwamnati ko aikin wata da iyaye mata suke yi a wannan zamani wanda hakan a wasu lokuta ke barazana ga irin kulawan da ‘ya’ya suke samu.

    Shirin Najeriya A Yau zai yi Nazari ne kan irin kalubalen da iyaye ke fuskanta a wannan zamani wajen tarbiyyan ‘ya’yan su.

    Domin sauke shirin, latsa nan


    [ad_2]

    Source link

  • Yau Shugabannin Tsaron Afrika 54 za su yi taro a Abuja

    [ad_1]



    A yau Litinin Najeriya take karbar baukuncin Shugabannin tsaron kasashen Afirka 54 a binrin Abuja, inda za su tattauna hanyoyin magance matsalolin tsaro da suka addabi nahiyar.

    Za a gudanar da taron ne a karkashin jagorancin Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, kuma Shugaban Kasa Bola Tinubu zai bude shi.

    Janar Musa ya ce taron, wanda shi ne na farko irinsa, zai bai wa shugabannin soji na Afirka damar tattauna matsalolin tsaro a fili tare da tsara hanyoyin magance su ba tare da dogaro da kasashen waje ba.

    “Mun dade muna neman mafita daga waje, abin da ya kara tsawaita matsalolinmu. Magana ta gaskiya ita ce, mafita tana cikinmu, mu ne za mu samar da ita,” in ji Janar Musa.

    Ya ce taron zai kuma duba batun rundunar sojin hadin gwiwar kasashen Afirka wadda har yanzu ba ta samu cikakken tsari ba, saboda matsalolin kudi da tsasre-tsare.

    Fiye da kashi 90 cikin 100 na kasashen da aka gayyata sun tabbatar cewa za su halarci taron , kana manyan jami’an Majalisar Dinkin Duniya da tsoffin hafsoshin tsaro da kwararru a harkokin tsaro za su halarta.

    Musa ya ce burin taron shi ne ganin nahiyar Afirka ta samu tsaro da ci gaba da kuma wanda ’ya’yanta ke jagorantar makomarta.


    [ad_2]

    Source link

  • Ƙungiyar KSCI Ta Nemi Sabon Tsari Don Magance Ƴan Bindiga A Katsina

    [ad_1]

    Ƴan asalin jihar Katsina a ƙarƙashin ƙungiyar Katsina Security Community Initiative (KSCI) sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da su fito da sabon tsari domin kawo ƙarshen matsalar ƴan bindiga da ta addabi jihar.

    Katsina ta ci gaba da fuskantar hare-haren ta’addanci inda ƴan bindiga ke mamaye ƙauyuka, suna kashe jama’a da yin garkuwa da su don neman kuɗin fansa. Wannan lamari ya tilasta ɗaruruwan mutane barin gidajensu, wasu kuma sun shiga yarjejeniyar sulhu da ƴan ta’adda domin tsira.

    Shugaban KSCI, Dr. Bashir Kurfi, ya bayyana a taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Abuja cewa kashe-kashen da sace mutane na ƙara tabbatar da cewa dabarun da ake amfani da su yanzu sun kasa magance matsalar. Ya ce fiye da rabin ƙananan hukumomin jihar suna hannun ƴan bindiga, lamarin da ya sa tafiye-tafiye cikin jihar ya zama hadari.

    Haka kuma, shugaban ƙaramar hukumar Safana, Abdullahi Sani Safana, ya ce yankinsa ya samu ɗan sassauci sakamakon tattaunawa da shugabannin al’umma da na addini, amma ya nuna damuwa cewa maƙwabtansu da ba su ɗauki irin wannan mataki ba suna kawo tarnaki ga ci gaba.

    A nasa ɓangaren, Farfesa Usman Yusuf Bugaje ya gargadi gwamnati cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, matsalar za ta iya bazuwa zuwa manyan birane a jihar.

    A ƙoƙarin gwamnati, rundunar sojin Nijeriya ta sanar da shirin kafa sabuwar bataliya a ƙaramar hukumar Malumfashi domin ƙarfafa yaƙi da tashe-tashen hankulan ƴan bindiga a jihar Katsina.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Ya kamata a dakakar da hadimin Gwamnan Kano — Ƙungiyoyi

    [ad_1]



    Gwamnatin Jihar Kano ta yi shiru yayin da wasu ƙungiyoyin farar hula suka buƙaci ta dakatar da manyan jami’abta da ake zargi da almundahana ta biliyoyin naira tare da gurfanar da su a gaban kotu.

    Wani rahoto na kafar yaɗa labarai ta Daily Nigerian ya bayyana cewa hukumomin ICPC da EFCC masu ya ki da almundahana sun gano badaƙalar Naira biliyan 6.5 da ake zargin Abdullahi Ibrahim Rogo, Darakta Janar na Al’amuran Kula da Baƙi a Fadar Gwamnatin Kano.

    Takardun da kafar ta ambato cewa ta samu suna zargin almundahanar ta faru ne tsakanin watan Nuwambar 2023 da Fabrairun 2025 ta hanyar kwangilolin bogi da sunan kamfanonin H&M Construction Nigeria Ltd, A.Y. Maikifi Petroleum da Ammas Oil & Gas Ltd.

    Sai dai duk ƙoƙarin jin ta bakin gwamnatin jihar ya ci tura, yayin da Kwamishinan Watsa Labarai, Ibrahim Wayya da Sakataran Gwamna ba su ɗauki kiran waya ba, kuma Darakta Janar na Watsa Labarai na Gwamnan, Sunusi Bature ya yi bukaguro zuwa ƙasar waje.

    Wannan dambarwar na zuwa ne bayan rahoton jaridar Nigerian Tribune a watan Yuli 2025, wanda ya bayyana cewa ICPC ta kammala bincike kan badaƙalar Naira biliyan 1.02 da ake zargin jami’an Hukumar Zaɓe ta Jihar Kano (KANSIEC).

    A wata sanarwa da wasu ƙungiyoyin fararen hula 20 suka sa hannu, sun yi gargaɗi cewa zarge-zargen na iya ɓata amincewar jama’a da gwamnati, tare da sare gwiwar masu zuba jari daga ƙasashen waje da kuma durƙushewar da ci-gaban jihar.

    “Wannan ba ƙaramin lamari ba ne. Ya nuna tsarin almundahana ta hanyar amfani da muƙaman gwamnati don amfanin kai,” in ji ƙungiyoyin.

    Sun kuma buƙaci a dakatar da duk jami’an da ake zargi tare da gudanar da bincike mai zaman kansa kan dukkanin ma’aikatun gwamnati.

    Haka kuma sun buƙaci Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ƙarfafa aikin sa ido tare da kafa dokar kare waɗanda ke fallasa rashawa.

    “Zaɓi yana a hannunmu: ko mu yaƙi rashawa mu dawo da martabar shugabanci ko kuma mu bari ta ƙara zurfi har ta kai ga rugujewar cibiyoyinmu da makomar ’ya’yanmu,” in ji sanarwar.


    [ad_2]

    Source link