Category: Latest News

  • Ɗan Nijeriya Ya Lashe Lambar Azurfa A Gasar Ninkaya Ta Duniya

    [ad_1]

    Wani matashin ɗan Nijeriya mai shekaru 17, Abdul Jabar Adama, ya lashe lambar azurfa a gasar ninkayar matasa ta duniya da aka yi a ƙasar Romania.

    Wannan shi ne karon farko da Nijeriya ta taɓa samun irin wannan lambar yabo a tarihin gasar.

    A gasar da ta ɗauki kwanaki shida, Adama ya samu lambar azurfa a tseren ninkaya na mita 50, inda ya kammala a cikin daƙiƙi 23.64.

    Ya zo na biyu bayan da ɗan Birtaniya, Dean Fearn, wanda ya lashe zinariya da daƙiƙa 23.54.

    Ba wai kawai ya samu lambar yabo ba, Adama ya kuma karya tarihin Nijeriya sau biyu a rana guda.

    Matashin, wanda yake yin atisaye a makarantar Mount Kelly ta Birtaniya, ya nuna cewa Nijeriya na da ƙwarewa a harkar ninkaya, duk da cewa har yanzu babu ɗan wasan ninkayar Nijeriya da ya taɓa kai wa gasar Olympics.

    Nijeriya dai ta taɓa lashe lambobin yabo 27 a wasannin Olympics amma ba ta taɓa yin nasara a fannin ninkaya ba.

    Hukumar wasanni ta kasa ta taya shi murna, tare da hukumar kula da wasannin ruwa ta Najeriya. Darakta Janar, Bukola Olopade, a cikin sanarwarsa a ranar Lahadi, ya ce wannan babbar nasara ce ga wasannin Najeriya baki ɗaya.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Yadda Hausawa Ke Tunƙaho Da Harshensu A Faɗin Duniya

    [ad_1]

    Duk shekara, ranar 26 ga watan Agusta ana gudanar da bikin Ranar Hausa ta Duniya, domin girmama da kuma ɗaukaka Harshen Hausa, wanda yake ɗaya daga cikin manyan harsunan Afirka da ake amfani da shi a sassa daban-daban na duniya.

    Wannan rana an fara ta ne a shekarar 2015, wanda fitaccen ɗan jarida Abdulbaqi Aliyu Jariya shirya domin wayar da kan al’umma game da darajar harshen Hausa, musamman a kafafen sada zumunta.

    Babban manufar wannan rana ita ce bunƙasa haɗin kai da fahimtar juna tsakanin masu amfani da harshen Hausa.

    Ana kuma jan hankalin jama’a kan yi amfani da harshen Hausa a rubuce-rubuce, a tattaunawa da mu’amala, musamman a shafukan sada zumunta.

    Wannan ya sa ake ganin Ranar Hausa ta Duniya a matsayin wata hanya ta kare harshen da kuma ƙarfafa amfani da shi a fannoni na zamani kamar kimiyya, fasaha da kasuwanci.

    Bikin ranar ba iya Nijeriya kawai ya tsaya ba. Ana gudanar da bikin a ƙasashe da dama irin su Ghana, Amurka, Turkiyya da kuma Dubai, inda al’ummar Hausawa ke yin rayuwa.

    A waɗannan wurare, ana shirya wasanni irin gargajiya kamar wasan Dambe, nuna abinci da kayayyakin al’adu, da kuma gudanar da taruka, tattaunawa kan harshen Hausa da tarihinsa.

    A Nijeriya, cibiyoyi da ƙungiyoyi masu zaman kansu sukan shirya taruka da laccoci.

    A jami’o’i irin su Jami’ar Bayero ta Kano da sauransu, masana da ɗalibai su kan tattauna kan ci gaban Hausa a fannin kimiyya da fasaha, da kuma ƙirƙiro sababbin kalmomi da ke dacewa da zamani.

    Haka kuma, jama’a na amfani da wannan rana a kafafen sada zumunta domin wallafa karin magana, hotuna da kayan al’adu, ko kuma rubuce-rubuce da ke nuna tumbatsar harshen Hausa.

    Al’ummar Hausawa da ke ƙasashen waje su kan yi shagulgula da suka haɗa da rawa, waka, da sauran nau’ikan nishaɗi na gargajiya, abin da ke ƙara ƙarfafa zumunci a tsakaninsu.

    Ranar Hausa ta Duniya ba ta zama lokaci na tunawa da harshen Hausa kaɗai ba, har ma da al’adu, kasuwanci da tarihin yadda harshen ya haɗa mutane da dama.

    Ita ce rana da ke nuna alfahari da asali, tare da nuna irin rawar da Hausa ta taka wajen bunƙasa ilimi da ci gaban zamani.

    Wannan yana ba da damar kallon harshen Hausa a matsayin abub alfahari da ya kamata a kula da shi tare da bunƙasa a nan gaba.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Anyi Carkin M’am na Al’ada Na Sco 2025 a Beijing

    [ad_1]

    Albarkacin taron koli na 25 na shugabannin kasashe membobin Kungiyar Hadin Kai Ta Shanghai (SCO), rukunin gidan rediyo da talibijin na Sin wato CMG, da sakatariyar kungiyar SCO sun shirya wani bikin hadin gwiwa na mu’ammalar al’adu a yau Litinin a Beijing.

    Shugaban Kyrgyzstan Sadyr Nurgozhoevich Japarov, da firayim ministan Pakistan Muhammad Shahbaz Sharif sun aike da sakon taya murnar cimma nasarar bikin. Kazalika, fitattun mutane daga fannonin siyasa, al’adu, da kafofin watsa labarai na kasashen SCO sama da 100 sun halarci taron, sun kuma shaida kaddamar da ayyuka da dama na mu’ammalar al’adu tsakanin kasashen kungiyar.

    Yayin taron, CMG da sakatariyar SCO sun yi musanyar takardun hadin gwiwa. Har ila yau, bangarorin biyu za su kafa hanyoyin sadarwa na dogon lokaci, don kara karfafawa da kuma zurfafa hadin gwiwarsu, musamman a fannonin fasahar zamani kamar ta AI da sauransu. (Amina Xu)




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Ba Da Kariya Shi Ne Tuna Baya—-Shekaru 80 Bayan Yakin Duniya Na II

    [ad_1]

    Tuna baya na nufin kara neman ci gaba cike da kyakkyawan burin. Shekaru 80 ke nan bayan yakin duniya na II, amma dan Adam na kan wata hanya mai muhimmanci na zabi tsakanin hadin kai ko rabuwar kawuna, tattaunawa ko fito na fito, moriyar juna ko nasara daga faduwar wani.

    Wani nazarin da kafar CGTN ta gudanar, wanda mutane 11,913 daga kasashe sama da 40 suka amsa ya nuna cewa, goyon bayan sakamakon nasarar yakin duniya na II da tsarin duniya bayan yakin ya samu karbuwa matuka.

    Nazarin ya nuna cewa, kaso 62.1 na mutane a fadin duniya sun yi imanin cewa, kare sakamakon yakin duniya na II abu ne mai matukar muhimmanci wajen tabbatar da odar duniya bayan yakin. Haka kuma, wasu kaso 67.9 sun amince cewa tsarin tafiyar da harkokin duniya karkashin MDD shi ne ginshinkin tabbatar da oda a duniya bayan yakin, kuma wannan batu ne da daukacin mutanen da suka bayar da amsa a nazarin, daga dukkan kasashen 40 suka amince da shi.

    Kimanin kaso 58 na masu bayar da amsa sun yi imanin cewa odar duniya bayan yakin yana lalacewa, inda kaso 58.9 kai tsaye suka bayyana Amurka a matsayin babbar mai haifar da tsaiko ga oda a duniya.

    Kafar CGTN da jami’ar Renmin ne suka gudanar da nazarin ta hannun cibiyar inganta tuntubar juna tsakanin kasa da kasa a sabon zamani. An kuma gudanar da nazarin ne tsakanin mutanen manyan kasashen duniya da na kasashe masu tasowa. (Fa’iza Mustapha)




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Gwamnatin Tarayya Ta Sake Gargadin Jihohin Arewa 9 Kan Afkuwar Ambaliya

    [ad_1]

    Cibiyar Gargadi ta Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya (FEW Centre) ta sake fitar da sanarwar gargadin ambaliyar ruwa ga Adamawa da wasu jihohi takwas na Arewa.

    Wata takardar da ke dauke da sa hannun Darakta mai kula da zaizayar kasa da ambaliyar ruwa, Usman Abdullahi Bokani, a Abuja ranar Litinin, ta bayyana cewa akwai yiwuwar wasu kauyukan Arewa za su fuskanci ruwan sama mai karfin gaske wanda zai iya haifar da ambaliya a tsakanin ranakun 25 zuwa 29 ga watan Agustan 2025.

    Bokani, wanda ya yi kira ga ma’aikatansa da ke cibiyoyin ma’aikar a jihohin da abun ya shafa da su bayar da rahoto kan duk wani sauyin yanayi a jihohinsu, ya kuma bayyana cewa, jihohin Bauchi, Gombe, Jigawa, Kano da Katsina, na gaba-gaba kan yiwuwar Afkuwar ambaliyar.

    Sauran jihohin da za a iya ganin ambaliyar ruwa a cikin lokacin hasashen sun hada da Sokoto da Zamfara.

    Jihohin Adamawa da Katsina ne ke da mafi yawan garuruwan da ake tsammanin ambaliyar.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • HOTUNA: Yadda aka karɓi baƙuncin Tinubu a Brazil

    [ad_1]



    A wannan Litinin ɗin Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sauka a Brasilia da ke ƙasar Brazil, inda ya fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu, domin amsa gayyatar da ƙasar ta yi masa.

    Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga shugaban Brazil, Inacio Lula da Silva, inda aka yi masa faretin ban girma irin na soji da ake karrama shugabannin ƙasashe.

    Ana saran shugabannin biyu da jami’ansu za su tattauna a kan batutuwa da dama da suka shafi sufurin jiragen sama da noma da harkar ma’adinai.

    Kazalika, shugabannin biyu za su tattauna inganta haɗakar diflomasiyya da sauran abubuwan da suka ce zai amfani ƙasashen biyu.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya Bayo Onanuga ya fitar, ya ce akwai alaƙa mai kyau tsakanin Najeriya da Brazil, inda ya ce a watan Maris na 2025, ƙasashen biyu sun ƙulla yarjejeninyar inganta noma da kasuwanci da tsaro da makamashi da ilimi da ma’adinai.

    A kwanakin baya, mataimakin shugaban ƙasar Brazil ya ziyarci Najeriya, inda ya kwashe kwanaki biyu yana tattaunawa kan batutuwa da dama da suka haɗa da noma da samar da taki da taraktoci da kuma bunƙasa masana’antu.


    [ad_2]

    Source link

  • ECOWAS Za Ta Kaddamar Da Rundunar Yaki Da Ta’addanci Mai Jami’ai 260,000

    [ad_1]

    Shugaban kungiyar ECOWAS, Omar Alieu Touray, ya bayyana shirin da kungiyar ke yi na kaddamar da rundunar soji mai jami’ai 260,000 domin yaki da ta’addanci a yankin Afirka.

    Touray ya bayyana hakan ne a wajen taron hafsoshin tsaro na kasashen Afirka na 2025 mai taken: “Yaki da barazanar da ake fuskanta a wannan zamani ga zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka: rawar da hadin gwiwar tsaro za ta haifar” wanda aka yi ranar Litinin a Abuja.

    Shugaban ECOWAS, wanda kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro, Ambasada Abdel-Fatau Musah ya wakilta, ya ce, kungiyar na bukatar dalar Amurka biliyan 2.5 don samar da kayan aiki da kuma tallafin kudi ga sojojin da za a tura kasashen da ke fama da ‘yan ta’adda.

    LEADERSHIP ta bayar da rahoton cewa, kasashe 36, daga cikin kasashe 54 na Afirka ne suka halarci taron.

    Yayin da wakilin Jamhuriyar Nijar ya yi na’am da wannan shirin amma, Mali da Burkina Faso ba su halarci taron ba wanda watakila hakan ba zai rasa alaka da rikicin siyasa tsakanin kasashen Sahel da ECOWAS ba.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Za A Watsa Shirin “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” A Manyan Kafofin Watsa Labarai Na Kasashen SCO

    [ad_1]

    Albarkacin taron koli na Kungiyar Hadin Kan Shanghai (SCO) na 2025, an yi bikin kaddamarwa na kasashen SCO, da shiri mai taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” da CMG ta shirya a yau Litinin a nan birnin Beijing. Tun daga yau, za a fara watsa shirin a manyan gidajen talibijin na Rasha, Kazakhstan, Kyrgyzstan, Pakistan, Iran, da Belarus da sauransu.

    Shugaban CMG Shen Haixiong ya bayyana cewa, shirin ya zabi labarai masu ban sha’awa na yadda Shugaba Xi Jinping ke kula da al’adu da ci gabansu, don bayyana muhimman ra’ayoyinsa game da al’adu. A karkashin ruhin “Shanghai”, za a ci gaba da rubuta sabon labari na hadin kai da rabon makoma tsakanin al’adu, tare da kafa kyakkyawar makoma ta bil’adama ta bai daya. (Amina Xu)




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Gwamnatin Kano ta musanta karkatar da N6.5bn daga baitul-malin jihar

    [ad_1]



    Gwamnatin Kano ta musanta rahotannin da ke zarginta da karkatar da Naira biliyan 6.5 daga baitul-malin jihar, tana mai cewa labarin “ƙarya ne da ‘yan adawa suka kitsa domin ɓata mata suna.”

    Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Litinin.

    Sanarwar ta ce labarin da aka wallafa a wani shafin yanar gizo a ranar 22 ga watan Agusta, wani yunƙuri ne na ɓata sunan gwamnatin da kuma lalata martabar jami’anta kafin Zaɓen 2027.

    Sanarwar ta ce taƙaddamar wadda a yanzu haka tana gaban kotu ta shafi Babban Darektan Tsare-Tsare (DG Protocol) na Gidan Gwamnati, Abdullahi Ibrahim Rogo, inda ta jaddada cewa nauyin da aka ɗora wa ofishinsa aiki ne na gudanarwa kawai kuma ba shi da ikon riƙon kuɗaɗen gwamnati kai tsaye.

    “Dukkan kuɗaɗen da ake fitarwa zuwa ma’aikatu da hukumomi ana yin su ne bisa kasafi da tsarin kuɗin gwamnati.

    “Babu wani mutum da ke riƙe kuɗin ma’akatu, hukumomi ko cibiyoyin gwamnati ba tare da dalilin da aka ware masa ba,” in ji sanarwar.

    Gwamnatin ta bayyana cewa Ofishin Protocol aikinsa ya haɗa da shirya jigilar gwamnati, walwala da jin daɗi, masauki, tafiye-tafiyen gwamna da kuma karɓar baƙi, ciki har da jakadu da manyan baƙi. Kuma saboda irin nauyin da yake ɗauka, ofishin kan sarrafa manyan kuɗaɗe amma ƙarƙashin amincewar gwamna ne kacokam.

    Sanusi Bature ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta jajirce wajen gaskiya, riƙon amana da adalci, kuma ba za ta yarda a zubar da mutuncin jami’anta ta hanyar wata farfaganda ba.

    Ya zargi jam’iyyun adawa da suka ɗauki hayar masu ƙirƙirar ƙorafe-ƙorafe da yaɗa bayanan ƙarya kan jami’an gwamnatin NNPP.

    Sanarwar ta kuma tunatar da yadda gwamnatin baya ƙarƙashin Abdullahi Ganduje ta kashe fiye da N20bn ta hannun Ofishin Protocol tsakanin Fabrairu da Mayun 2023, ban da wasu zarge-zargen rashawa da ake yi mata.

    “Mutanen Kano har yanzu ba su manta da bidiyon dala na tsohon gwamna kuma shugaban riƙon jam’iyyar APC ba,” in ji sanarwar.

    Gwamnatin ta yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su kiyaye ka’idojin aikin jarida su guji zama masu ruɗar da jama’a.

    Ta ce ba ta da abin ɓoyewa, kuma jami’anta a shirye suke su amsa tambayoyin hukumomin yaƙi da cin hanci duk lokacin da ake buƙata.

    Sanarwar ta ƙara da cewa, “Wannan zargi ƙarya ne da ’yan adawa suka kitsa a matsayin farfaganda domin neman suna a siyasance.”

    Ta jaddada cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf na mayar da hankali kan mulkin nagari, tattalin dukiyar jama’a da inganta rayuwar al’umma, tare da gargaɗin ’yan adawa da cewa idan suka ci gaba da yaɗa bayanan ƙarya, za a ɗauki matakin shari’a a kansu.


    [ad_2]

    Source link

  • Zargin Babban Hadimin Gwamnan Kano Ya Karkatar Da Kuɗaɗen Jama’a Ba Gaskiya Ba Ne

    [ad_1]

    Gwamnatin jihar Kano ta musanta zargin cewa babban daraktan kula da harkokin gidan gwamnati, Abdullahi Ibrahim Rogo ya karkatar da naira biliyan 6.5 daga asusun jihar, inda ta bayyana ikirarin a matsayin siyasa.

    LEADERSHIP ta ruwaito cewa, zargin da wata jarida ta intanet ta rahoto a ranar 22 ga watan Agusta, ta bayyana cewa, Rogo ya cire kudaden ne tsakanin watan Nuwamba 2023 zuwa Fabrairu 2025 ta hannun kamfanoni, H&M Construction Nigeria Ltd, A.Y. Maikifi Petroleum, da kuma Ammas Oil and Gas Ltd.

    A cewar jaridar, an karkatar da kudaden ne ta hanyar wasu kwangiloli da ba a aiwatar da su ba.

    Amma, a cikin wata sanarwa mai kakkausar murya da ya fitar a ranar Litinin, Daraktan Yada Labarai na Gidan Gwamnati, Sanusi Bature DawakinTofa, ya karya rahoton da cewa “aiki ne na tatsuniyoyi, wadanda abokan hamayyar siyasa suka shirya su, domin bata wa gwamnati suna don su samu madafun iko gabanin zaben 2027.

    “Kowane tsabar kudi da ke fita a cikin Ma’aikatun gwamnati a tsare suke yadda ya kamata a cikin kundin kasafin kudi na jihar. Don haka, babu wani mutum a cikin gwamnati da ke kula da kudaden jama’a ba tare da wata manufa ta musamman ba,” in ji sanarwar.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link