Category: Latest News

  • Sin Ta Bukaci Japan Ta Waiwayi Tarihin Kutsen Da Ta Yi

    [ad_1]

    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta gabatar da korafi mai tsanani ga Japan, dangane da munanan kalaman da take yi game da katafaren taron da kasar Sin za ta yi, albarkacin cika shekaru 80 da al’ummar Sinawa ta yi nasara a yakin kin harin Japan da yakin duniya na II.

    Yayin taron manema labarai na yau Talata, kakakin ma’aikatar Guo Jiakun, ya ce manufar tunawa da ranar ita ce, tunawa da tarihi da kuma girmama zaman lafiya.

    Ya ce duk wata kasa da za ta kalli tarihin da daraja tare da daukar darasi, kuma take da burin neman ci gaba cikin lumana, ba za ta ki amincewa da shi ba.

    Ya ce fahimtar tarihi da daukarsa yadda ya kamata, muhimmin tubali ne na komawar Japan cikin harkokin kasa da kasa bayan yakin, kuma shi ne tubalin siyasa na raya dangantakarta da kasashe makwabta, haka kuma muhimmin ma’auni ne na gwada ko Japan za ta cika alkawarinta na neman ci gaba cikin lumana.

    Kakakin ya bukaci Japan da ta fuskanci tarihin ta kuma nazarci kutsen da ta yi, ta ajiye batun kara karfinta na soji a gefe, ta bi tafarkin neman ci gaba cikin lumana da girmama abun da ke zukatan al’ummar Sinawa da sauran kasashen da lamarin ya shafa. (Fa’iza Mustapha)




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 128 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Zamfara

    [ad_1]

    A yau Talata, 26 ga Agusta, 2025, jami’an tsaron Nijeriya sun samu damar kubutar da mutum 128 daga hannun ‘yan bindiga a Kaura Namoda ta Jihar Zamfara.

    An gabatar da mutanen da aka kuɓutar a ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, wanda ya bayyana lamarin a matsayin “babbar nasara a yaƙin da ake yi da rashin tsaro a Nijeriya.”

    Yayin da yake jawabi a gaban waɗanda aka ceto, Ribadu ya ce aikin bai tsaya kan kuɓutar da mutanen da aka kama kawai ba, har ma ya haɗa da lura da yanayin lafiyarsu da kuma tabbatar da an haɗa su da iyalansu cikin aminci.

    Ribadu ya yaba da jajircewar sojoji da ‘yansanda da sauran jami’an tsaro da suka gudanar da aikin, yana mai cewa, wannan wata nasara ce da za a yi alfahari da ita a tarihin yaki da ta’addanci.

    A Guji Siyasantar da Tsaro

    Sai dai Ribadu ya gargadi shugabannin siyasa da masu rike da madafun iko da su guji siyasantar da al’amuran tsaro, yana mai cewa:

    “Wannan ƙalubale na gama gari ne, ba wai na shugabanni kaɗai ba. Domin haka nake kira ga al’umma da shugabanni su daina siyasantar da tsaro.”

    Ribadu ya ƙara da cewa, gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu, za ta ci gaba da yin duk abin da ya kamata domin magance barazanar tsaro tare da kawo ƙarshen matsalar garkuwa da mutane a Nijeriya.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Xi Da Uwargidansa ​​Sun Gana Da Sarkin Cambodia Da Mahaifiyarsa Sarauniya

    [ad_1]

    A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan suka gana da Sarkin Cambodia Norodom Sihamoni, da mahaifiyarsa Sarauniya Norodom Monineath Sihanouk a birnin Beijing.

    Xi ya yi kyakkyawar maraba da zuwan Sarki Norodom Sihamoni da mahaifiyarsa Sarauniya Norodom Monineath Sihanouk kasar Sin, kana ya yi lale maraba da halartar Sarki Sihamoni bikin da za a yi na cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiyar jama’ar kasar Sin kan zaluncin kasar Japan, da kuma yaki da mulkin danniya a duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • An yi kiciɓus da gawar ’yar shekara 14 a cikin gida a Kano

    [ad_1]



    An yi kiciɓus da gawar wata budurwa mai shekaru 14 a cikin gidansu da ke unguwar Dandinshe a Ƙaramar Hukumar Dala da ke Jihar Kano.

    Lamarin dai ya ɗugunzuma mazauna unguwar yayin da Aminiya ta riski iyaye, ’yan uwa da kuma maƙwabta cikin alhini a yayin ziyarar da ta kai har gida.

    Bayanai sun ce an yi arba da gawar Fatima Sulaiman rataye a jikin wata taga a cikin gidansu, lamarin da ya jefa shakku da ayoyin tambaya kan musabbabin mutuwarta.

    Aminiya ta zanta da mahaifiyar marigayiyar, Malama Madina Inuwa Makwalla, wadda ta bayyana ganawa ta ƙarshe da ta yi da ’yarta.

    “A ranar Asabar da yamma, muna shirin kai ziyara asibiti domin duba wani ɗan uwanmu.

    “Da muka shirya tafiya, sai Fatima ta ce za ta shiga bandaki sannan ta biyo mu. Ashe ban sani ba, wannan ne karo na ƙarshe da zan gana da ita,” a cewar Madina tana faɗa cikin hawaye.

    Mahaifiyar ta bayyana cewa har suka dawo daga asibiti Fatima ba ta biyo su ba, inda suka tarar da ƙofar gidan an kulle ta daga ciki, kuma duk wani yunƙurin buɗewa da suka yi da safayar makullin da ke hannunsu ya ci tura.

    A wannan lokacin ne mahaifinta, Malam Sulaiman, wanda ya dawo daga kasuwa, ya haura ta katanga ya shiga gida, inda ya yi arba da abin da ba zai taɓa mantawa a rayuwarsa ba kamar yadda Malama Madina ta bayyana.

    “Ya tarar da ɗiyarmu a rataye, babu rai. Ya yi matuƙar firgita, nan da nan ya kira ni, wanda ihun da na yi ya ankarar da maƙwabta suka yi ta taruwa,” in ji Malama Madina.

    Mazauna unguwar da suka yi dandazon ganewa idanunsu wannan abun al’ajabi, sun bayyana shakku kan lamarin da cewa da yiwuwar akwai hannun wani, saboda alamu sun nuna an karya wuyanta kafin a rataye ta.

    Mahaifin marigayiyar ya tabbatar cewa nan take suka sanar da ’yan sanda, waɗanda suka iso wurin, suka ɗauki gawar zuwa Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad, inda likitoci suka tabbatar da cewa rai ya yi mata halinsa tun kafin su kawo ta.

    A cewarsa, “ba mu san wanda zai aikata wannan mummunan aiki ba. Amma muna kira ga hukumomin tsaro da su binciki lamarin sosai domin a gano masu hannu a ciki.

    “Mun bar wa Allah wannan lamari. Muna roƙonSa Ya tona asirin duk wanda ya aikata wannan laifi. Allah Ya sa Aljannah ce makomarta.”

    Kakakin rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa sun soma cikakken bincike domin gano haƙiƙanin abinda ya faru domin tabbatar da adalci.

    Maƙwabta da suka zanta da wakilinmu sun bayyana Fatima a matsayin yarinya mai ladabi, biyayya da girmama kowa.

    “An santa da mutunci da zaman lafiya da kowa a unguwa. Wannan mutuwa ta girgiza mu gaba ɗaya,” in ji wani maƙwabci.

    Tuni dai an binne gawar Fatima bisa koyarwar addinin Islama, inda ɗaruruwan jama’a suka halarci jana’izarta.


    [ad_2]

    Source link

  • Gwamna Uba Sani Ya Ba Da Umarnin Talllafawa Fasinjojin Da Ke Cikin Jirgin

    [ad_1]

    Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana matukar kaduwarta kan hatsarin da ya faru da jirgin kasa da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna, wanda ya afku a safiyar ranar Talata, wanda ya haifar da firgici a tsakanin fasinjoji da iyalansu.

    Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labarai, Malam Ahmed Maiyaki, ya fitar ranar Talata a Kaduna.

    Maiyaki ya kara da cewa, bayan rahoton faruwar lamarin, Gwamna Uba Sani nan take ya umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (SEMA) da Ma’aikatar Kananan Hukumomin Jihar da su gaggauta kai dauki ga fasinjojin da lamarin ya rutsa da su.

    Hukumar ta SEMA ta dauki nauyin kwashe fasinjojin da suka makale, da bayar da agajin gaggawa, da kuma tabbatar da cewa duk wadanda abin ya shafa sun samu kulawar gaggawa a inda ya dace.

    “Gwamnan ya ba da umarnin a baiwa fasinjoji duk wani tallafi da ya dace don rage tasirin wannan mummunan lamari, duk wanda ya samu rauni za a kula da shi cikin gaggawa, yayin da ake ba da tallafin gaggawa na psycho-socio da tallafin likita ga wadanda abin ya shafa,” in ji Maiyaki.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin jirgin, inda ta kara da cewa gwamnatin jihar na sanya ido sosai kan lamarin tare da hadin gwiwar hukumomin tarayya da masu ruwa da tsaki da abin ya shafa.

    Da safiyar ranar Talata ne muka rahoto muku cewa, jirgin kasa da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna, ya sauka a kan layin dogo jim kadan bayan ya bar tasharsa da misalin karfe 11 na safe, inda ya bar fasinjojinsa cikin firgici.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Muna Fatan Gaggauta Tabbatar Da Sakamakon Taron Beijing Na FOCAC

    [ad_1]

    Shugaban Kongo Brazzaville Denis Sassou Nguesso, ya bayyana a jiya Litinin 25 ga watan nan cewa, zai himmatu wajen sauke nauyin dake wuyan kasarsa, kasancewarta mai shugabancin hadin gwiwa na taron FOCAC, da kuma ingiza tabbatar da sakamakon taron Beijing cikin sauri.

    Sassou Nguesso ya bayyana hakan ne yayin ganawa da An Qing, jakadiyar Sin dake kasarsa. Ya ce, bayan shekaru 60 da kafa huldar diflomasiyya tsakanin kasarsa da Sin, kasashen biyu sun ci gaba da kasancewa abokai na kut da kut. Ya kuma shaida bunkasar huldar kasashen biyu. Ya ce Kongo Brazzaville na shirin kara habaka huldar abota da Sin, da kuma kara zurfafa hadin gwiwa, don inganta dangantakarsu da ma tsakanin kasashen Afrika da Sin.

    A nata bangare, An Qing ta ce, a karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, Sin da Kongo Brazzaville sun karfafa amincewa da juna, suna tallafa wa juna, kuma suna samun ci gaba tare. Kazalika, dangantakar kasashen biyu ta zama misali ga hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Kuma Sin na shirin kara karfafa abota ta gargajiya da kasar, da tabbatar da amincin siyasa, da kuma zurfafa hadin gwiwa a fannoni daban-daban. (Amina Xu)




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Hisbah ta haramta al’adun gargajiya yayin bukukuwan aure a Bauchi

    [ad_1]



    Hukumar Hisbah ta haramta karuwanci da duk wasu munanan ɗabi’u da ake gudanarwa a otal-otal, wuraren casu da duk wasu cibiyoyin nishaɗi a Jihar Bauchi.

    Babban Kwamishinan Hisbah, Barista Aminu Balarabe Isah, ya bayyana haka ne a yayin wani taron tattaunawa da masu otal-otal da wuraren shaƙatawa a Bauchi.

    Ya ce an haramta gudanar da al’adun gargajiya irin su Shadi, Sharo, Garaya da kuma shagulgulan wannan zamani kamar Kauyawa Day, Gala, DJ, Aloba da sauransu a bukukuwan aure.

    Isah ya ce an ɗauki waɗannan matakan ne bayan samun korafe-korafe daga jama’a kan yadda abubuwa na rashin tarbiyya da tayar da fitina ke ƙaruwa a faɗin jihar.

    Daga cikin dokokin da aka shimfiɗa akwai hana cakuɗuwar mata da maza, rawa tsakanin jinsi daban-daban tare da ƙananan yara.

    Haka kuma an hana fatauci ko shan barasa da miyagun ƙwayoyi, bukukuwan birthday da duk wasu ababe na yaɗa fasadi da ka iya tayar da tarzoma.

    Kazalika, sanarwar ta haramta caca, kallace-kallacen fina-finai na batsa a ko’ina da kuma jan hankali jama’a kan sanya tufafin da suka dace yayin zuwa wuraren nishaɗi.

    Ya yi kira da cewa za a dakatar da duk wasu harkoki a wuraren shaƙatawa da zarar lokacin sallah ya yi.

    Isah ya ce duk wanda bai kiyaye waɗannan ƙa’idoji ba, hukumar Hisbah za ta ɗauki matakin da ya dace a kansa.


    [ad_2]

    Source link

  • Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna Ya Yi Hatsari, Ba A San Halin Da Fasinjoji Ke Ciki Ba

    [ad_1]

    Jirgin ƙasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya yi hatsari da safiyar ranar Talata, lamarim da ya jefa fasinjoji da dama cikin hatsari.

    Hatsarin ya faru ne bayan jirgin ya bar Abuja da ƙarfe 11 na safe a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna.

    Wani fasinja da ya wallafa labarin a shafukan sada zumunta ya bayyana cewa fasinjoji sun na cikin firgici, inda mutane suka dinga gudu domin tsira da rayukansu.

    Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto Hukumar Jiragen Ƙasa ta Nijeriya (NRC), ba ta tabbatar da lamarin ba, kuma ba a san abin da ta haifar da hatsarin ba.

    Har ila yau ba a san halin da fasinjojin suke ciki ba.

    Dakarun tsaro sun isa wajen domin taimakawa wajen kwashe fasinjojin da kuma tabbatar da cewa babu matsalar tsaro a wajen.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Saka Zai Yi Jinyar Makonni 4 Sakamakon Rauni Da Ya Samu A Wasan Leeds

    [ad_1]

    Ɗan wasan gaban Arsenal, Bukayo Saka, ba zai iya buga wasan Arsenal da Liverpool na ranar Lahadi ba sakamakon raunin da ya samu.

    Haka kuma ba zai buga wasannin da ƙasarsa ta Ingila za ta yi da Andorra da Serbia da za a yi watan gobe ba.

    Saka mai shekaru 23 ya ji rauni a ƙafarsa a wasan da suka doke Leeds United a ranar Asabar, kuma likitoci sun ce zai ɗauki aƙalla makonni huɗu kafin ya dawo filin wasa.

    Haka nan akwai shakku kan ko Martin Odegaard, kyaftin ɗin Arsenal, zai buga wasan  Liverpool a filin Anfield.

    Shi ma ya samu rauni a kafaɗarsa a wasan da Arsenal ta doke Leeds da ci, inda kocin Arsenal Mikel Arteta ya cire shi a minti na 38.

    Har yanzu babu tabbaci ko zai iya buga wasan.

    Arsenal na fatan cewa Saka da Odegaard ba za su daɗe suna jinya ba.

    A kakar da ta wuce, Saka ya sha fama da rauni har ya yi watanni uku ba ya wasa.

    Sai dai a bana Arsenal ta ƙara wasu sababbin ‘yan wassan gaba kamar Viktor Gyokeres da Eberechi Eze, baya ga waɗanda ta ke da su kamar Gabriel Martinelli, Leandro Trossard, Ethan Nwaneri da Max Dowman don rage giɓin Saka da Odegaard.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • ‘Yan Kasuwa Na Neman Diyya Bayan Rushe Kasuwar Alaba Rago A Legas

    [ad_1]

    ’Yan kasuwar Alaba Rago da ke ƙaramar hukumar Ojo a Jihar Legas, wadanda yawancinsu daga Arewa suke, sun nemi gwamnatin jihar ta biya su diyya saboda rusau da aka yi musu.

    Sun ce an rushe musu shaguna da kayayyakinsu da suka kai na biliyonin naira, ba tare da sanarwa ba.

    Wasu daga cikin ’yan kasuwar sun zargi cewa an haɗa baki da jami’an gwamnati wajen aiwatar da rusau ɗin duk da yarjejeniyar da suka ce suna da ita da gwamnati.

    Wazirin Sarkin Alaba Rago, Alhaji Adamu Katagum, ya ce ba za su yarda a ƙwace musu dukiya da suka tara tun shekaru aru-aru ba.

    Haka kuma wasu ’yan kasuwar sun bayyana cewa rusau ɗin ya sa ɓata-gari sun sace musu kaya, wasu kuma sun ji rauni.

    Wasu daga cikin ’yan kasuwar sun yi kira ga gwamnati da ta sake duba matsayar ta, inda suka ce kasuwar ce tushen rayuwarsu da iyalansu, kuma rushe ta zai kara jefa su cikin talauci da rashin aikin yi.

    Haka kuma, sun yi barazanar kai ƙarar gwamnati kotu idan aka ƙi biyan su diyya, domin a cewarsu, an tauye musu haƙƙin kasuwanci da kuma dukiyar da suka shafe shekaru suna tarawa.

    Sai dai gwamnatin Legas ta ce irin waɗannan ayyuka na rusau na daga cikin shirinta na zamanantar da manyan kasuwanni, don su dace da tsarin birane na zamani da kuma kare muhalli.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link