Hisbah ta haramta al’adun gargajiya yayin bukukuwan aure a Bauchi

[ad_1]



Hukumar Hisbah ta haramta karuwanci da duk wasu munanan ɗabi’u da ake gudanarwa a otal-otal, wuraren casu da duk wasu cibiyoyin nishaɗi a Jihar Bauchi.

Babban Kwamishinan Hisbah, Barista Aminu Balarabe Isah, ya bayyana haka ne a yayin wani taron tattaunawa da masu otal-otal da wuraren shaƙatawa a Bauchi.

Ya ce an haramta gudanar da al’adun gargajiya irin su Shadi, Sharo, Garaya da kuma shagulgulan wannan zamani kamar Kauyawa Day, Gala, DJ, Aloba da sauransu a bukukuwan aure.

Isah ya ce an ɗauki waɗannan matakan ne bayan samun korafe-korafe daga jama’a kan yadda abubuwa na rashin tarbiyya da tayar da fitina ke ƙaruwa a faɗin jihar.

Daga cikin dokokin da aka shimfiɗa akwai hana cakuɗuwar mata da maza, rawa tsakanin jinsi daban-daban tare da ƙananan yara.

Haka kuma an hana fatauci ko shan barasa da miyagun ƙwayoyi, bukukuwan birthday da duk wasu ababe na yaɗa fasadi da ka iya tayar da tarzoma.

Kazalika, sanarwar ta haramta caca, kallace-kallacen fina-finai na batsa a ko’ina da kuma jan hankali jama’a kan sanya tufafin da suka dace yayin zuwa wuraren nishaɗi.

Ya yi kira da cewa za a dakatar da duk wasu harkoki a wuraren shaƙatawa da zarar lokacin sallah ya yi.

Isah ya ce duk wanda bai kiyaye waɗannan ƙa’idoji ba, hukumar Hisbah za ta ɗauki matakin da ya dace a kansa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *