Category: Latest News

  • Yanzu-yanzu: Jirgi kasan Kaduna-Abuja ya yi hatsari

    [ad_1]



    Jirgin kasa dauke da fasinjoji a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ya sauka daga kan titi.

    Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin tarogon jirgin kasan sun mirgina a yayin da fasinjoji suka shiga tashin hankali.


    [ad_2]

    Source link

  • Mutane Na Neman Diyya Bayan Rushe Kasuwar Alaba Rago A Legas

    [ad_1]

    ’Yan kasuwar Alaba Rago da ke ƙaramar hukumar Ojo a Jihar Legas, wadanda yawancinsu daga Arewa suke, sun nemi gwamnatin jihar ta biya su diyya saboda rusau da aka yi musu.

    Sun ce an rushe musu shaguna da kayayyakinsu da suka kai na biliyonin naira, ba tare da sanarwa ba.

    Wasu daga cikin ’yan kasuwar sun zargi cewa an haɗa baki da jami’an gwamnati wajen aiwatar da rusau ɗin duk da yarjejeniyar da suka ce suna da ita da gwamnati.

    Wazirin Sarkin Alaba Rago, Alhaji Adamu Katagum, ya ce ba za su yarda a ƙwace musu dukiya da suka tara tun shekaru aru-aru ba.

    Haka kuma wasu ’yan kasuwar sun bayyana cewa rusau ɗin ya sa ɓata-gari sun sace musu kaya, wasu kuma sun ji rauni.

    Wasu daga cikin ’yan kasuwar sun yi kira ga gwamnati da ta sake duba matsayar ta, inda suka ce kasuwar ce tushen rayuwarsu da iyalansu, kuma rushe ta zai kara jefa su cikin talauci da rashin aikin yi.

    Haka kuma, sun yi barazanar kai ƙarar gwamnati kotu idan aka ƙi biyan su diyya, domin a cewarsu, an tauye musu haƙƙin kasuwanci da kuma dukiyar da suka shafe shekaru suna tarawa.

    Sai dai gwamnatin Legas ta ce irin waɗannan ayyuka na rusau na daga cikin shirinta na zamanantar da manyan kasuwanni, don su dace da tsarin birane na zamani da kuma kare muhalli.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Yadda bikin Ranar Hausa ta Duniya ke gudana a Fadar Sarkin Daura

    [ad_1]



    A halin yanzu Sarkin Daura, ya hallara a filin gagarumin bikin Ranar Hausa ta Duniya da a bana ake gudanarwa a fadarsa, inda za a gudanar da hawan daba na musamman.

    Sarkin Daura ya karbi bakuncin Gwamnan Jihar Damagaram daga Jamhuriyar Nijar, Kanar Yosouf Labo da kuma Sarkin Damagaram, Aboubacar Sanda Oumarou a fadarsa, albarkacin bikin Ranar Hausa ta Duniya.

    Ga kadan daga cikin hotunan yadda kasaitaccen bikin ke gudana.


    [ad_2]

    Source link

  • Ɗaruruwan ‘Yan APC Sun Koma ADC A Sakkwato Saboda Rashin Tsaro Da Talauci

    [ad_1]

    Ɗaruruwan mambobin jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Gada ta Jihar Sakkwato, sun fice daga jam’iyyar, tare da komawa jam’iyyar ADC.

    Sun ce sun bar APC ne saboda matsalar tsaro, talauci, da kuma rashin kyakkyawan shugabanci.

    An karɓe su a hukumance a ranar Lahadi ta hannun Sanata Abubakar Gada, ɗaya daga cikin manyan shugabannin haɗakar ADC.

    Ya ce wannan lamari alama ce ta yadda mutane da dama ke gamsuwa da rashin nagartar gwamnatin APC.

    “Mutanenmu na fama da matsanancin rashin tsaro wanda ya lalata noma, wanda shi ne ginshiƙin tattalin arziƙinmu. Wannan ya jawo talauci, rashin aikin yi da yunwa a cikin al’umma,” in ji Gada yayin taron.

    Ya ƙara da cewa jama’a na shiga ADC saboda suna ganin ita ce mafita.

    “Gazawar gwamnatin APC ta tilasta mutane su nemi mafita, kuma ADC za ta bayar da wannan damar,” in ji shi.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • ECOWAS na shirin kafa rundunar yaki da ta’addanci mai dakaru 260,000

    [ad_1]



    Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka ta ECOWAS ta bayyana shirinta na kafa rundunar yaki da ta’addanci mai dauke da sojoji 260,000 domin tunkarar barazanar tsaro da ke kara ta’azzara a yankin.

    Shugaban ECOWAS, Omar Alieu Touray, wanda wakilinsa Abdel-Fatau Musah ya gabatar da jawabi a taron shugabannin rundunonin tsaro na Afirka da aka gudanar a Abuja, ya ce wannan mataki na daga cikin kokarin dakile ayyukan ta’addanci da sauran matsalolin tsaro da suka addabi yankin.

    “Babu wani yanki a Afirka da ya tsira daga ta’addanci, rikice-rikicen cikin gida da kuma koma-baya ta fannin ci-gaba,” in ji Musah.

    ECOWAS ta ce za ta bukaci dala biliyan 2.5 a kowace shekara domin tallafa wa rundunar da kayan aiki da kudaden gudanarwa. Ana sa ran Ministocin kudi da na tsaro za su gana a ranar Juma’a domin kammala tsarin yadda za a samar da kudaden.

    Touray ya ce yankin Sahel ya fi kowanne yanki fama da ta’addanci, inda ya ce kashi 51 cikin 100 na mutanen da suka mutu sakamakon ta’addanci a duniya a shekarar 2024 sun fito ne daga yankin.

    A yayin da ECOWAS ke ci gaba da kokarin kafa rundunar sojoji 5,000 karkashin tsarin tsaro na Afirka, ana sa ran sabuwar rundunar za ta taimaka wajen kara karfin yaki da ta’addanci.

    Sai dai ba dukkan kasashen da aka gayyata suka halarci taron ba. Daga cikin kasashe 54 da aka gayyata, 36 ne suka samu wakilci.

    Ko da yake Jamhuriyar Nijar ta halarta, Mali da Burkina Faso ba su halarta ba — lamarin da ba zai rasa nasaba da rikicin siyasa da ke tsakaninsu da ECOWAS ba.

    Tsohon Firaministan Guinea, Lansana Kouyaté, ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin mataki na hadin gwiwar tsaro a Afirka.

    “Karon farko ne shugabannin rundunonin tsaro na dukkan kasashen Afirka suka hadu. Wannan ya nuna muhimmancin batun — ba za a samu ci gaba ba sai da zaman lafiya,” in ji shi.

    Kouyaté ya bukaci shugabannin Afirka da su hada kai wajen samar da tsaro, yana mai jaddada cewa Afirka ba kasa daya ba ce, illa dai hadin gwiwar kasashe masu bambancin tarihi da al’adu. Ya ce zai gabatar da shawarwari kan yadda za a samar da kudaden tsaro ta hanyar hadin gwiwa da masu zaman kansu.

    A nata bangaren, Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed, ta bukaci shugabannin Afirka da su dauki nauyin tsaron nahiyar.

    Ta yi gargadin cewa ta’addanci, yaki ta kafar intanet da sauyin yanayi na barazana ga zaman lafiyar Afirka. Ta kara da cewa, “Afirka ta zama cibiyar mutuwar mutane sakamakon ta’addanci. A cikin shekaru biyu kacal, hare-hare a kasashen gabar tekun yammacin Afirka sun karu da kashi 250 cikin 100.”

    Ta ce fiye da makarantu 14,000 sun rufe a yankin Sahel saboda rikici, sannan ta yi gargadi kan barazanar fasahar zamani da sauyin yanayi, ciki har da faduwar ruwan tafkin Chadi da ta raba fiye da mutane miliyan uku da muhallinsu.

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, wanda Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta, ya bukaci a samar da sabuwar dokar tsaro ta nahiyar Afirka da za ta dogara da amincewa, musayar bayanan sirri da hadin gwiwa.

    “Wannan taro bai kamata ya kare da tafi ba kawai watse. Ya zama ginshikin sabuwar tsarin tsaro na Afirka,” in ji shi.

    Ya bukaci a kafa taron dindindin na shugabannin rundunonin tsaro na Afirka da kuma zuba jari a fannin kirkire-kirkire na tsaro da fasahar zamani.

    A karshe, tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya bayyana cewa akwai fiye da kungiyoyin ’yan tada kayar baya 1,000 a nahiyar Afirka, yana mai kira da a kara karfafa masana’antar tsaro da kirkirar fasahohin gida.


    [ad_2]

    Source link

  • Yadda shirye-shiryen babban bikin Ranar Hausa ta Duniya ke gudana

    [ad_1]



    Yau 26 ga watan Agusta take ranar murnar zagayowar bikin Ranar Hausa ta Duniya.

    A halin yanzu shirye-shirye sun yi nisa domin fara gagarumin bikin Ranar Hausa ta Duniya a birnin Daura, Jihar Katsina.

    An shirya gudanar da gagarumin bikin na bana a birnin Daura ne, kasancewarsa inda ake gani a matsayin asalin Hausawa, shekaru arau-aru.

    Mahaya dawaki da sauran mahalarta bikin daga sassa daban-daban na Najeriya da kasashen waje da mazauna garin Daura sun fara tururuwa zuwa filin bikin, wanda zai samu.

    An kuma shirya gudanar da gagarumin hawan daba a Fadar Sarkin Daura, albarkacin zagayowar bikin Ranar Hausa ta Duniya karo na 10.

    A wannan ranar ake cika shekara 10 da fara wannan gagarumin biki, wanda a bana zai gudana a kasashe 26.

    Makada da mahaya saura masu sana’o’in gargajiyar Hausawa sun fara kayatar da ’yan kallo da kade-kade da bushe-bushe da sauransu, a wannan kasaitaccen biki.


    [ad_2]

    Source link

  • ASUU Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Rashin Cika Mata Alƙawura

    [ad_1]

    Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU), reshen Akure, ta gargaɗi gwamnatin tarayya da kada ta tilasta musu shiga yajin aiki sakamakon matsalolin jami’o’i ke fuskanta.

    Da yake jawabi a taron manema labarai a Jami’ar Tarayya, Oye-Ekiti (FUOYE), Shugaban ASUU na jami’ar, Farfesa Adeola Egbedokun, ya ce malaman sun yi haƙuri sama da shekaru biyu ba tare da yin yajin aiki ba, suna jiran gwamnati ta cika musj alƙawura.

    “Haƙurinmu ya kusa ƙarewa,” in ji shi, yana mai cewa malaman sun yi babbar sadaukarwa amma gwamnati ba ta yi abin da ya kamata ba.

    Ya bayyana bukatun ASUU da suka haɗa da:

    • Sake duba yarjejeniyar ASUU da Gwamnatin Tarayya ta 2009.
    • Soke tsarin rancen ɗalibai na TISSF da ASUU ke ganin zai jefa ɗalibai cin bashi.
    • Dakatar da kafa sababbin jami’o’i ba tare da tsari ba.
    • Inganta fanshon malamai da sauran ma’aikata.

    Egbedokun ya zargi gwamnati da ɓata lokaci da kuma yin alkawuran karya.

    “Mun yi tattaunawar gaskiya, amma gwamnati tana yi mana wasa,” in ji shi.

    Ya ce an yi watsi da rahotanni masu muhimmanci, an kafa manufofin da ke cutar da ilimi, sannan an jefa malaman da suka yi ritaya mummunan hali.

    “Wannan gwamnati ta raina ilimi da malamai. Mun gaji,” in ji shi.

    Shugaban ASUU ya yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta ƙi ɗaukar mataki, za ta ɗauki alhakin duk wata matsala da za ta biyo baya.

    Ya kuma kira mambobin ASUU da su fito ƙwansu da kwarkwata wajen tarukan da za a gudanar a manyan jami’o’i a ranar Talata, 26 ga Agusta, 2025, yana mai cewa wannan shi ne mataki na farko da ƙungiyar za ta ɗauka don nuna rashin amincewa da halin da gwamnati ta shiga.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Yau ake cika shekaru 10 da ƙirƙirar Ranar Hausa

    [ad_1]



    A duk ranar 26 ga watan Agustan kowace shekara ake bukukuwan zagayowar Ranar Hausa ta Duniya.

    An fara wannan biki ne tun a shekarar 2015, inda wani tsohon ma’aikacin sashen Hausa na BBC kuma ma’aikacin TRT Hausa a yanzu, Abdulbaƙi Jari Aliyu ya ƙirƙiro tare da wasu masu amfani da shafukan sada zumunta.

    An ɓullo da ranar ce domin haɗa kan masu magana da harshen Hausa a faɗin duniya da nufin magance matsalolin da ke ci musu tuwo a ƙwarya.

    Da farko dai, an fara bikin wannan rana ce kamar wasa a shafukan sada zumunta, inda aka yi ta amfani da kalmar #RanarHausa. Zuwa shekara ta 2018 kuma aka fara yin bikin a zahiri tare da gudanar da tarurruka da shagulgula a garuruwa a faɗin Najeriya da ma wasu ƙasashen irinsu Ghana.

    Masu shirya bikin ranar suna ƙoƙarin ganin sun bayyana mahimmancin harshen Hausa da yadda za a ci gaba da yaɗa shi. Haka kuma a kan tattaro masana da masu bincike domin yin nazari kan wasu sabbin abubuwa da ya kamata a sani da Hausa.

    A shekaru biyu da suka shuɗe, an yi bikin Ranar Hausa ta Duniya a ƙasashe sama da 20, ciki har da Faransa da Saudiyya.

    Masu fafutukar wannan rana suna fatan cewa nan gaba za a amince da yaren Hausa a hukumance a ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) da kuma ƙungiyar raya ƙasashen yammacin Afrika (ECOWAS).

    Wane ci-gaba aka samu?

    A wannan shekarar dai za a yi gagarumin bikin wannan rana a garin Daura da ke Jihar Katsina, wajen da ake kallo a matsayin tushen Hausa da al’ummar Hausawa.

    Za a yi tattaunawa da kuma nuna al’adu tare da mahalarta daga ƙasashe daban-daban a yammacin Afirka da kewaye.

    Abdulbaƙi Aliyu Jari, wanda shi ne jagoran wannan taro na Ranar Hausa ta Duniya, ya shaida wa Aminiya cewa, a yanzu haka bincike ya ayyana harshen Hausa a matsayin yare na 11 da ake aka fi amfani da shi a faɗin duniya, kuma ana sa ran nan da shekarar 2050 zai zama na biyar a duniya.

    “Hausa ba kamar sauran yaruka ba ne da suke ɓacewa, Hausa na ƙara bunƙasa. Ana magana da yaren a nahiyar Afirka tsakanin mutane fiye da miliyan 170,” in ji shi.

    Ya bayyana cewa, Hausa ya riga da ya samu gurbi na musamman a Jamhuriyar Nijar, inda kaso sama da 80 na al’ummarsu ƙasar suke magana da yaren, haka ma a ƙasar Ghana. Kafofin yaɗa labarai ma tuni suka rungumi harshen Hausa domin isar da saƙonninsu ga ɗimbin mabiya a faɗin duniya.

    Jari ya ce, sun faro wannan lamari ne kamar wasa a shekarar 2015, amma sai ga shi yanzu duk duniya ana maganar sa. “Abu ne da aka faro a shafukan sada zumunta, sai ga shi yanzu ana bikin a ƙasashe kusan 25”.

    A cewar Jari, Ranar Hausa ta Duniya, “Ba wai biki ba ce kawai, a’a, wata hanya ce da masu magana da harshen Hausa a duk faɗin Najeriya, Afirka ta Yamma da sauran ƙasashen duniya za su haɗa kai, su tattauna ƙalubalen da ke damun su da kuma samar da zaman lafiya.”

    Da yake tsokaci kan nasarorin da aka samu a cikin shekaru goma da suka gabata, ya bayyana cewa a halin yanzu bikin ranar Hausa ya samu wani gurbi  a kalandar masu magana da harshen Hausa a duk duniya.

    Jari ya yi kira ga gwamnatocin Afirka, musamman a Najeriya da Afirka ta Yamma, da su amince da Hausa a matsayin harshen ƙasa ko na yanki a hukumance, ta hanyar yin koyi da Jamhuriyar Nijar inda ake magana da Hausa a hukumance.

    Hakan a cewarsa zai yara al’adu taro da tabbatar da wanzuwar zaman lafiya.

    Su wane ne Hausawa?

    Ana kallon al’ummar Hausawa a matsayin ɗaya daga cikin ƙabilu masu muhimmanci a yammacin Afirka, da al’adunsu na musamman a faɗin nahiyar da ma sauran ƙasashen duniya. Yayin da wasu alƙaluma suka ce adadin Hausawa ya kai kimanin miliyan 150, Farfesa Muhammad Bunza na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sakkwato na ganin cewa adadin zai iya haura miliyan 500 idan aka haɗa da masu magana da yare biyu.

    Ba a iya Najeriya ake samun al’ummar Hausawa ba, baya ga Nijar akwai ƙasashe irin su Saudiyya, Sudan, Maroko, Libya, da Mali, inda suke zuwa kasuwanci, ko kuma a kan haɗu ta dalilin auratayya.

    A wata hira da BBC Hausa a shekarar 2023, Farfesa Bunza ya  bayyana cewa tsawon shekaru aru-aru, auratayya tsakanin ƙabilu da Hausawa ta sa su rikiɗewa zuwa ƙabila guda.

    A yanzu dai, harshen Hausa yana cikin jerin harsunan da ake magana da su a duniya, inda wasu suka ce na bakwai a duniya, kuma yana ci gaba da samun karɓuwa. Amma duk da haka, Farfesa Bunza ya yi gargaɗin cewa harshen yana fuskantar ƙalubale, ciki har da ƙarancin koyar da shi a makarantu da rashin malamansa.

    Ya buƙaci gwamnatocin Afirka da su haɓaka amfani da harshen, yana mai cewa, “Baya ga Swahili, babu wani yare na Afirka da zai iya yin gogayya da Hausa.

    Yadda yaren Hausa ya bunƙasa

    Masana harshe da dama na yi wa harshen Hausa kallon wani harshe mai yaɗuwa a faɗin duniya, inda yanzu haka nazarce-nazarce ke nuna cewa Hausa ne harshe na 11 a fadin duniya wajen yawan masu amfani da shi, kuma na ɗaya a Afirka ta yamma.

    Sai dai akwai jayayya tsakanin manazarta kan girman Hausa a nahiyar Afirka, inda wasu ke ganin harshen Swahili da ake yi a ƙasashe da dama na yankin Afirka maso Gabas ya ɗara na Hausa wanda ake yi a yankin Afirka ta yamma da Afirka ta Tsakiya da ma kusurwar Afirka.

    Sai dai nazarce-nazarce sun nuna harshen Hausa yana gaba da na Swahili ta fannin yawan masu yin amfani da shi inda shi kuma Swahili ke gaba wajen yawan ƙasashen da ake yin yaren.

    Tuni dai manyan kafafe irin su Facebook da Google suke amfani da harshen Hausa inda tuni manhajar amfani ta Android da IOS suka shigar da shi cikin harsunan da suke amfani da su.

    Ko a baya-bayan nan sai da hukumar Lafiya ta Duniya ta sanya Hausa a cikin harsuna guda uku da ta zaɓa domin yaki da annobar korona a Afirka.


    [ad_2]

    Source link

  • Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka

    [ad_1]

    Wannan takarda gudunmuwa ce ga al’umma masu kishin harshen Hausa, domin a gyara matsalolin da ke damunsa musamman koma bayansa a jami’o’i.

    Takardar ta kawo matsalolin, ta bayyana gudunmuwar harshen, sannan ta bayar da shawara ta yadda za a inganta shi.

    Har ila yau, ta tattaro wasu bayanai daga abin da malamai suka riga suka yi.

    Amma fahimta daban-daban ake da ita, ni a mahangata zan yi bayani ta fuskoki uku.

    Na sa mata suna “Ba Ka Iyawa, Duk Dagewarka, Ba A Yaba Maka (Dankali Sha Kushe)” saboda irin ƙalubalen da harshen yake fuskanta daga gwamnati, malamai, da al’ummar Hausawa da ke jan kafa ga masu nazartar harshen duk da gudunmuwar da suke bayarwa ga al’umma, gwamnati da addini.

    Na yi imani babu rayuwa ba tare da harshe ba, domin duk wata al’umma tana da buƙatar harshe domin gudanar da rubuce-rubuce, kimiyya da fasaha.

    Amma an yi sakaci da nazarin harshen Hausa, duk da cewa yana cikin manyan harsunan duniya masu ƙarfi da adabi.

    Don haka zan fara bayyana matsalolin, sannan in kawo shawarwari.

    Matsala ta farko: Sai Bango Ya Tsage…

    Idan gwamnati da manyan al’umma ba su ɗauki Hausa da muhimmanci ba, ba zai samu ci gaba ba. An taɓa samun shugaban ƙasa da ya ce nazarin wasu darusa ɓata lokaci ne, amma shi kansa a lokacin yaƙin neman zaɓe da Hausa yake magana.

    Gwamnati ta nuna rashin kulawa da harshen Hausa, tana ganin ba shi da amfani. Alal misali:

    1. Mayar da Hausa “zaɓi” a sakandire.

    2. Tsaurara sharuɗa wajen shiga jami’a domin nazartarsa.

    3. Rashin bayar da tallafin karatu kamar yadda ake yi wa wasu harsuna.

    Matsala ta biyu: Ka Ƙi Naka, Duniya Ta So Shi

    Da yawa daga cikin Hausawa ba sa alfahari da harshensu. Maimakon su zurfafa a kansa, sai ƙasashen waje suka ɗauki Hausa suna koyarwa a jami’o’in duniya. Haka kuma, yawancin Hausawa idan suna amfani da shafukan sada zumunta, rubuce-rubucensu da Hausa suke yi, ko littattafan addini sai an fassara musu da Hausa.

    Abin kunya ne a ce ƙasar Nijar ta ayyana Hausa a matsayin harshen ƙasa, amma Nijeriya ba ta yi haka ba, duk kuwa da cewa Hausa na daga cikin manyan harsunan ƙasar.

    Haka kuma wasu malamai suna sa wa ɗalibai wahala wajen nazarin Hausa, suna ƙauron da su daga koyonsa.

    Matsala ta uku: Idan An Bi Ta Ɓarawo…

    Ya kamata malamai da ɗalibai su ci gaba da aikin fassara kalmomi daga fannoni daban-daban na ilimi zuwa Hausa, don a samu damar shiga kowanne fanni kamar yadda ake yi da Turanci, Larabci, Sinanci da sauransu.

    Gudunmuwar Harshen Hausa:

    1. An fassara kusan duk littattafan addini zuwa Hausa.

    2. An fassara littattafan kimiyya, tarihi, lissafi da sauransu.

    3. Hausa ta mamaye kafafen sada zumunta kamar Facebook, WhatsApp, X, Instagram da TikTok.

    4. Ana amfani da Hausa a kafafen yaɗa labarai a ƙasashe irin su Amurka, Sin da Faransa.

    5. Malamai sun rubuta littattafai da muƙaloli da dama domin ci gaban harshen.

    Shawarwari:

    1. A tafiya da zamani wajen koyar da Hausa.

    2. A sauƙaƙa hanyoyin koyo da koyarwa.

    3. A mayar da Hausa darasi na dole a firamare da sakandire.

    4. A wajabta wa ɗaliban ƙasashen waje koyon Hausa idan suka zo karatu a Nijeriya.

    5. A shigar da Hausa cikim fannin kimiyya da fasaha.

    6. A sa Hausa cikin darussan GES/GSE a jami’o’i da kwalejojin ilimi.

    7. A ayyana Hausa a matsayin harshen hukuma a Arewa ko Nijeriya baki ɗaya.

    8. A ƙarfafa gwiwar iyaye, abokai da malamai ga ɗaliban da ke nazartar Hausa.

    9. A riƙa bai wa masanan Hausa aikin da ya dace da su, musamman fassara da rubuce-rubuce.

    Idan aka aiwatar da waɗannan, za a dawo da martabar harshen Hausa.

    Kammalawa

    Takardar ta nuna matsalolin da harshen Hausa ke fuskanta, gudunmuwar da yake bayarwa ga al’umma da addini, sannan ta kawo hanyoyin da za a bi don dawo da martabarsa a ƙasar nan.

    Mubarak Idris Jikamshi ne ya rubuta albarkacin Ranar Hausa ta Duniya




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • NAJERIYA A YAU: Ci Gaban Da Harshe Da Al’adun Hausa Suka Samu A Shekaru 10

    [ad_1]

    Karin fannoni



    Tun bayan fara bikin harshen Hausa ta duniya shekaru goma da suka gabata ne dai manazarta suke bayyana irin cigaba da habbakar da yaren ya samu.

    Harshen Hausa ya samu zama a mataki na 11 cikin harsunan da ake amfani dasu a fadin duniya tare da fatan nan bada jimawa ba zai dara hakan.

    Shirin Najeriya  A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin cigaba ko akasin haka da harshen Hausa da aladunta suka samu cikin shekara goma.

    Domin sauke shirin, latsa nan


    [ad_2]

    Source link