Category: Latest News

  • Wani Rahoton Kasar Sin Ya Kalubalanci Halaccin Ayyukan Amurka Bisa Dogaro Da “’Yancin Zirga-zirga”

    [ad_1]

    Cibiyar lura da harkokin teku ta kasar Sin dake karkashin ma’aikatar kula da albarkatu ta kasar, ta fitar da wani rahoto dake kalubalantar halaccin Amurka na gudanar da ayyuka bisa dogaro da “’yancin zirga-zirgar jiragen ruwa”.

    Rahoton wanda aka fitar jiya, ya bayyana batun “‘yancin zirga-zirga” na Amurka a matsayin wanda ke tattare da ka’idoji da dokokin da Amurkar ta tsara da kan ta, wadanda suka saba da dokokin kasa da kasa da yadda kasashe da dama ke tafiyar da harkokinsu.

    Ya ce abun da Amurka ke kira da “‘yancin zirga-zirga”, ba ya bisa doron dokar kasa da kasa, kuma yana lalata fassarar dokar da ma aiwatar da ita. Ya kuma bayyana cewa, matakin misali ne na abun da Amurka ta saba yi na dogaro da karfin soja wajen matsawa sauran kasashe lamba.

    Har ila yau, rahoton ya ce, matakin na Amurka muradu da dabarunta na siyasar duniya kadai yake karewa, yayin da take dogaro da karfin soja wajen haifar da tsaiko ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankuna da ma tsarin harkokin tekun na duniya. Bugu da kari, ya soki ayyukan Amurka yana cewa, sun saba doka, ba su kamata ba, kuma suna nuna fuskoki biyu. (Fa’iza Mustapha)




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • PDP ta miƙa wa kudancin Najeriya takarar shugaban ƙasa a 2027

    [ad_1]



    Babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya, PDP, ta keɓe wa kudancin Nijeriya tikitin takarar kujerar shugaban ƙasa a Zaɓen 2027.

    Jam’iyyar ta tabbatar da haka ne a babban taron Kwamitin Zartarwa karo na 102 da ta gudanar ranar Litinin a Abuja.

    A baya-bayan nan dai wasu masu ruwa da tsaki kan sha’anin siyasa sun zafafa kiraye-kiraye ga tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya yi wa jam’iyyar takara a Zaɓen 2027.

    A yayin taron na yau ne kuma PDP ta tabbatar da Umar Damagum a matsayin shugabanta na ƙasa a hukumance.

    Damagum wanda ya shafe fiye da shekara guda a matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar a yanzu ya zama shugaba mai cikakken iko gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasa da za a gudanar a ranakun 15 a 16 ga watan Nuwamba a birnin Ibadan na Jihar Oyo.

    A watan Maris ɗin 2023, PDP ta naɗa Damagum a matsayin shugaban riƙo, bayan dakatar da shugabanta na wancan lokacin, Sanata Iyorchia Ayu.


    [ad_2]

    Source link

  • Burkina Faso Da Mali Sun Yi Watsi Da Taron Sojojin Afirka A Nijeriya

    [ad_1]

    Burkina Faso da Mali ba su tura wakilai zuwa taron soja na nahiyar Afirka da Nijeriya ta shirya a ranar litinin ba, yayin da alakar kasashen Sahel da ke karkashin mulkin soja da kuma makwabtansu na yammacin Afirka ke ci gaba da tsami.

    Nijar Mali da Burkina Faso da ke karkashin mulkin soja, sun fice daga kungiyar ECOWAS a watan Janairu, bayan da suka kafa nasu kawancen kasashen Sahel (AES) yayin da suka dade suna fafatawa da mayakan jihadi da suka addabi yankin na Sahel.

    Nijar, wacce mai kula da tsaron ofishin jakadancin kasar, Kanar Soumana Kalkoye ya wakilta, ita ce kasa daya tilo ta AES a taron shugabannin hafsoshin tsaron Afirka, da aka shirya a Abuja, babban birnin Nijeriya.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Beijing Zai Bunkasa Amfani Da Fasahohin Zamani A Wuraren Adana Kayan Tarihi

    [ad_1]

    Mahukuntan birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, sun sha alwashin inganta bincike, da amfani da fasahohin zamani don kyautata gabatar da abubuwa, da wuraren tarihi na birnin nan zuwa shekarar 2035.

    Hukumar lura da kayayyakin tarihi ta birnin ce ta bayyana hakan, tana mai cewa shirin da aka yi domin cimma nasarar hakan, zai kunshi amfani da kirkirarriyar basira ko AI, da runbun manyan bayanai, da fasahar VR a gidajen adana kayan tarihi, da wuraren da ake killacewa tarihinsu.

    Hukumar ta kara da cewa, za a kirkiri cikakken tsarin tattara bayanai na dijital mai kunshe a dukkanin kayan tarihi da ba a iya sauyawa wuri, ta hanyar amfani da bayanai daga jerin binciken da aka gudanar a matakin kasa na yanzu da wanda ya gabata. Kana za a yi amfani da sabbin abubuwa, da fasahohin kare tsaffin gine-ginen itatuwa daga lalacewa.

    A daya bangaren kuma, za a yiwa gidajen baje kayayyakin tarihi babban garan bawul. Karkashin hakan, za a rika amfani da fasahar nuna bidiyo ta VR, domin baiwa masu ziyarar gidajen damar ganin abubuwan dake ajiye tamkar a gaske. Har ila yau, za a karfafa amfani da intanet, da AI domin inganta tsaron kayayyakin tarihi da tsarin kare su daga lalacewa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • PDD ta tabbatar da Damagum a matsayin shugabanta na ƙasa

    [ad_1]



    Kwamitin Zartaswa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar adawa ta PDP ya tabbatar da Umar Damagum a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa.

    Wannan dai na zuwa ne a yayin zaman NEC na 102 da ke gudana a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja.

    A jawabinsa na karɓar shugabanci, Damagum ya gode wa sauran mambobin Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) bisa taimako da haɗin kai da suka ba shi wajen gudanar da aikinsa.

    Ya kuma gode wa mambobin NEC bisa yabawa da amincewa da ƙoƙarinsa wajen farfaɗo da jam’iyyar, abin da ya ce hakan ya taimaka wajen tabbatar da shi a matsayin shugaban jam’iyyar.


    [ad_2]

    Source link

  • Rashin Tsaro: Ana Ƙoƙarin Ganin Ƙarshen Haƙurin Arewa

    [ad_1]

    Dandalin Tuntuɓa na Arewa (ACF) ya yi gargaɗin cewa, ana ƙoƙarin ganin ƙarshen haƙurin Arewacin Nijeriya biyo bayan ta’azzarar matsalar rashin tsaro da talauci da kuma annobar muhalli da yankin ke fuskanta.

    Dandalin ya yi wannan gargadin ne a yayin babban taron kwamitin zartarwa na ACF karo na 78 da ya gudanar a Kaduna.

    Shugaban Dandalin, Mamman Osuman, wanda ya yi jawabi a wurin taron, ya ce Arewa ba za ta iya yin shiru ba a yayin da yankin ke fama da irin wannan kalubalen da “ya ƙi ci ya ƙi cinyewa”.

    Ya kuma yi gargadin cewa, “Wannan ba lokaci ba ne da Arewa za ta naɗe hannunta tana kallo yayin da al’amura ke ci gaba da taɓarɓarewa, lamarin tsaro yana kara ta’azzara yayin da ake ci gaba da kwashe albarkatun yankin, ambaliyar ruwa na ci gaba da barazana, dole ne mu tashi tsaye mu hada kai domin kare yankin.”

    Osuman ya koka da kashe-kashen da ake yi a Arewacin Nijeriya a kullum, yana mai jaddada cewa, babu yadda za a yi, a zura ido ana kallo.

    “Mun yi asarar yara, matasa maza da mata, da tsoffi saboda ambaliyar ruwa, bala’o’i, ‘yan bindiga da masu kwacen wayoyi, halin da ake ciki, akwai matukar damuwa, don haka nake kira da a yi tunani mai zurfi kan nemo mafita da kuma addu’a,” in ji shi.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Wata mata ta mayar da N4.8m da aka yi kuskuren tura wa asusunta a Maiduguri

    [ad_1]



    Wata mata mai aikin shara da goge-goge, Fa’iza Abdulkadir, ta mayar da kuɗi har N4.8m da aka yi kuskuren tura wa asusun bankinta a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

    Da take zantawa da News Central a Maiduguri, Fa’iza wadda take ɗaukan albashin Naira dubu 30 duk wata ta ce ta yanke shawarar mayar da kuɗin ne saboda tsoron Allah.

    “Wannan kuɗi ba haƙƙi na ba ne, ba ni na mallaki kuɗin ba, shi ya sa na mayar. Na fi son na zauna cikin kwanciyar hankali da kuma gudun azabar Allah a ranar lahira,” in ji ta.

    Fa’iza ta bayyana cewa ta shafe kwanaki uku tana zaraya a banki kafin ta kammala duk matakan mayar da kuɗin.

    “Na shafe kwanaki uku babu sukuni don ko abincin kirki ba na samu na ci yadda kamata har sai da na mayar da kuɗin, sannan na samu kwanciyar hankali,” in ji ta.

    Ma’aikatan banki da maƙwabta a unguwar da take zaune sun bayyana Fa’iza a matsayin mace mai gaskiya wadda take rayuwa da albashin N30,000 da take samu daga wata cibiyar lafiya inda take aiki.

    “Ba abin mamaki ba ne, saboda yadda take da tarbiyya da kuma yadda take renon ‘ya’yanta.

    “Tana da kyawawan ɗabi’u, kuma tana rayuwa cikin rufin asiri da ‘ya’yanta guda biyar,” in ji wata maƙwabciyarta.

    Wani jami’in banki ya ce abin da Fa’iza ta yi ya ba mutane mamaki sosai. “Duk da halin da take ciki, ta ji tsoron Allah ta yi abin da ya dace.

    “Na taɓa ganin irin haka ta faru a wannan banki inda aka yi kuskuren tura kuɗi a asusun wani, ya cire kuɗin ya kashe.

    “Sai da ya jefa ma’aikatan banki cikin tashin hankali don hatta ‘yan sanda sun shiga lamarin, amma har yanzu ba a dawo da kuɗin ba,” in ji shi.


    [ad_2]

    Source link

  • Sin Ta Shiga Jerin Kasashe 3 Dake Sahun Gaba Wajen Gudanar Da Cinikayya Da Kasashe Da Yankunan Duniya 157

    [ad_1]

    Shugabar hukumar kwastam ta kasar Sin Sun Meijun, ta ce Sin ta shiga jerin kasashe uku dake sahun gaba wajen gudanar da cinikayya da kasashe da yankunan duniya 157.

    Sun Meijun, ta bayyana hakan ne a Litinin din nan yayin taron manema labarai da ta gudana, inda ta ce a shekarar 2024 darajar hada-hadar cinikayya tsakanin Sin da kasashen da suka shiga shawarar ziri daya da hanya daya ta kai yuan tiriliyan 22, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan uku, ciki har da wadanda suka hada da sama da kaso 50 bisa dari na jimillar hada-hadar shige da ficen hajoji. (Mai fassara: Saminu Alhassan)




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • An yaudari ’yan Nijeriya da suka hana Jonathan lashe Zaɓen 2015 — Ƙungiya

    [ad_1]



    Wata ƙungiyar siyasa da ke goyon bayan masu fafutikar nan ta “Bring Back Our Goodluck” ta buƙaci tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, da ya tsaya takara a Zaɓen 2027.

    Ƙungiyar ta ce a Zaɓen 2015 an yaudari ‘yan Najeriya da suka dage wajen ganin bai yi nasara ba a ƙoƙarinsa na neman wa’adi na biyu, lamarin da yanzu kowa yake nadama saboda an jefa ƙasar cikin tsanani da tsadar rayuwa da rashin tsaro.

    A yayin wani taro na Arewa maso Yamma da aka gudanar ranar Lahadi a Kano, madugun ƙungiyar na ƙasa, Dokra Grema Kyari, ya bayyana cewa lokaci ya yi da Jonathan zai dawo ya “ceci Najeriya daga matsin tattalin arziƙi da rashin zaman lafiya.”

    Ya zargi jam’iyyar APC da shugabanninta a wancan lokaci, ciki har da marigayi Muhammadu Buhari da Bola Ahmed Tinubu, da yi wa al’ummar Najeriya alƙawura na bogi.

    Ƙungiyar ta jero dalilai huɗu da ta ce sun wajabta dawowar Jonathan da suka haɗa da samar da zaman lafiya, inganta tattalin arziƙi, shugabanci na haɗin kai da kuma kima a idon duniya.

    Kyari ya yi nuni da cewa a zamanin Jonathan buhun shinkafa kilo 50 bai wuce N7,800 ba, amma yanzu yana kaiwa N80,000–N100,000.

    Ya kuma ce manufofin gwamnatinsa kamar YouWin!, SURE-P da shirin bunƙasa noma sun amfani matasa da mata.

    Ƙungiyar ta roƙi manyan ‘yan adawa kamar Atiku Abubakar, Rabi’u Musa Kwankwaso, Peter Obi da su haɗa kai su mara wa Jonathan baya a 2027, tana mai cewa “Zaɓen 2027 aikin ceto ne.”


    [ad_2]

    Source link

  • Za a yi amfani da Hausa wajen samar da zaman lafiya — Abdulbaqi Jari

    [ad_1]



    Za a yi amfani da harshen Hausa a matsayin hanyar samar da zaman lafiya a yayin bikin Ranar Hausa ta Duniya karo na goma (10), wanda za a gudanar a Daura da ke Jihar Katsina, a ranar Talata, 26 ga watan Agusta, 2025.

    Jagoran taron, Abdulbaqi Aliyu Jari, wanda shi ne ya ƙirƙiri wannan rana, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Katsina.

    Ya ce dukkan shirye-shirye sun kammala, kuma manyan baƙi daga ciki da wajen Najeriya tuni sun fara isowa domin halartar bikin.

    Jari ya ce an tsara taron ne domin baje kolin al’adun Hausawa da kuma jaddada muhimmancin harshen Hausa a matsayin alamar alfahari da haɗin kai.

    A cewarsa, za a yi baje kolin kayan tarihi da dama, ciki har da hawan doki, sana’o’in gargajiya, saƙa da sauran su, domin nuna gadon al’adu da darajar harshen Hausa.

    Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihohi da su ƙara bai wa harsunan asali dama, musamman Hausa wanda mutum fiye da miliyan 200 ke amfani da shi a duniya.

    Ya ƙara da cewa lokaci ya yi da Hausa za ta samu ƙarin ƙarfafawa a matsayin harshen ƙasa a hukumance, duba da yaɗuwar harshen musamman yadda ya ƙetare iyakokin Najeriya zuwa wasu ƙasashen Afirka ta Yamma, ƙasashen ECOWAS da maƙwabta.

    “Idan aka amince da Hausa a matsayin harshen ƙasa, hakan zai ƙara sauƙaƙa mu’amala, ya bunƙasa kasuwanci, ya inganta alaƙa tsakanin jama’a, tare da taimakawa wajen samar da zaman lafiya,” in ji shi.

    Taken bikin na bana shi ne: “Amfani da Harshen Hausa Don Samar da Zaman Lafiya.”

    Abdulbaqi ya bayyana cewa manufar babban taron shi ne ƙarfafa fahimtar juna da wayar da kan jama’a kan rawar da harshen Hausa da al’adun Hausawa za su iya takawa wajen wanzar da zaman lafiya.

    Kazalika, Jari ya ce ana sa ran halartar gwamnoni, ministoci, sarakunan gargajiya da manyan baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar, tare da kira ga jama’a daga nesa da kusa da su hallara a Daura domin shaida baje kolin al’adun Hausawa a idon duniya.


    [ad_2]

    Source link