Boko Haram sun nemi N423m kuɗin fansar mutanen da suka sace a Borno
[ad_1]
’Yan ta’addan Boko Haram da suka yi garkuwa da wani kansila da tsohon mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Biu a Jihar Borno a kwanakin baya, sun buƙaci kuɗi har naira miliyan 423 kafin sakin mutanen da suka sace.
Hakan na zuwa ne bayan bayyanar wani sabon bidiyo da ke nuna mutane biyu da ake zargin ’yan Boko Haram/ISWAP ne suka sace a Jihar Borno, inda suke neman taimakon Gwamnatin Borno da sauran al’umma domin ceto su daga hannun ’yan ta’addan.
A cikin bidiyon, an ga ɗaya daga cikin waɗanda aka sace, Honarabul Hassan Biu Miringa, tsohon mataimakin shugaban Ƙaramar Hukumar Biu, yana roƙon gwamnati da jama’a da a taimaka wajen ceto su.
An yi garkuwa da mutanen biyu ne a ranar 17 ga Disamba, 2025, yayin da suke tafiya daga Miringa zuwa Maiduguri.
’Yan ta’addan sun bayyana cewa suna neman dala 150,000 kan kowane mutum, jimilla dala 300,000, wanda ya yi daidai da naira miliyan 423 a kuɗin Najeriya, domin sakin su.
“An sace mu ne a kan hanyarmu daga Miringa zuwa Maiduguri da misalin ƙarfe 2:30 na rana. Alhamdulillah, muna raye,” in ji ɗaya daga cikin waɗanda aka sace.
“Muna kira ga gwamnati da ɗaiɗaikun mutane da su taimaka wajen ceto mu.”
Mutanen da aka sace sun yi kira musamman ga Mataimakin Gwamnan Borno, Umar Usman Kadafur, da Mukhtar Betara Aliyu, Sule Ali Rimi, Yakubu Gambo Kimba, da Alhaji Musa Dogo Biu, da su shiga lamarin domin taimakawa wajen tabbatar da ’yancinsu.
“Muna roƙonsu da su zo su cece mu. Mu ’ya’yansu ne,” in ji su.
“Sun ce dole ne kowannenmu ya biya dala 150,000. Mu biyu ke nan dala 300,000 ake nema. Muna fatan sake haɗuwa da iyalanmu.”
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link