Fashewar tankar mai ta jikkata mutane da dama a Legas
[ad_1]
An ba da rahoton gobarar fashewar wata tankar mai ɗauke da man fetur a jihar Legas wanda hakan ta raunata wasu mazauna yankin.
Lamarin ya faru ne da safiyar Alhamis a kan titin Abeokuta, a cewar shaidu, an ga ragowar man a cikin magudanun ruwa yana ci da wuta a yankin.
Rahotanni sun bayyana cewa mazauna yankin sun yi dafifi don ɗibar man, duk da gargaɗin da ma’aikatan gaggawa da suka yi.
Babban Sakatare na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA), Dakta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce, hatsarin ya rutsa da wata tankar mai ta dizal ce mai cike da mai, inda ta kife sannan ta kama da wuta a kan titin Abeokuta zuwa cikin garin Agege.
“Ta kama gobarar, yayin da sauran man da ya zube da ke ci a magudanun ruwa ya kama da wuta. Ba a samu rahoton wanda ya rasa ransa ba. Wani ɗaya ya samu rauni kuma yana karɓar magani,” in ji shi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link