Mutane 5 Sun Rasu, 35 Sun Jikkata A Harin Bam A Masallaci A Borno


Wani ɗan ƙunar baƙin wake ya kai hari wani masallaci a Kasuwar Ngamboru, yayin da ake yin sallar Magariba a ranar Laraba, inda ya kashe mutane biyar tare da jikkata wasu 35.

Harin ya auku ne da misalin ƙarfe 6:10 na yamma, inda ya haddasa tashin hankali a yankin.

  • AFCON 2026: Algeria Ta Lallasa Sudan Da Ci 3 Da Nema
  • Dangote Kaɗai Ba Zai Iya Wadatar Da Nijeriya Man Fetur Ba, In Ji Manyan ‘Yan Kasuwa

An kai waɗanda suka ji jikkata zuw Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH) da sauran asibitoci.

‘Yansandan Jihar Borno sun tabbatar da faruwar harin, inda suka ce ana ci gaba da bincike.

An rufe wajen don tabbatar da tsaron jama’a.

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi Allah-wadai da harin.

Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, kuma ya yi kira da ƙara tsaurara tsaro a wuraren ibada musamman a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.

Shaidu sun ce maharin ya shiga masallacin ne yayin sallar Magariba.

Harin ya lalata wasu sassan rufin masallacin kuma ya jefa kasuwar da ke kusa da masallacin cikin firgici.

Ofishin gwamna Zulum, ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Dauda Iliya, ya ce gwamnatin jihar na sake duba matakan tsaro don hana aukuwar irin wannan hari, musamman a wuraren da jama’a ke taruwa.

‘Yansanda sun ce tawagar binciken bama-bamai, tana bincike a yankin domin gano sauran abubuwan fashewa da za su iya zama barazana ga mutane.

Gwamna ya yi kira ga al’umma da su kasance masu sanya ido sa kuma kai rahoton duk wani abun zargi ga hukumomi.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *