Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 16, Sun Ceto Mutane 11 A Borno
Sojojin rundunar hadin gwiwa (Arewa maso Gabas), ‘Operation HADIN KAI’ (OPHK), sun kashe ‘yan ta’adda 16 a kan titin Gidan Kaji na hanyar Maiduguri zuwa Damboa a jihar Borno.
Sojojin sun kuma gano babura sama da 20, tarin alburusai, da makamai, da sauran kayayyaki da ake kyautata zaton suna da matukar muhimmanci ga ayyukan ta’addanci.
A cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na hedikwatar rundunar hadin gwiwa ta ‘Operation HADIN KAI’, Laftanar Kanar Sani Uba ya fitar a ranar Laraba, ta ce, an ceto mutane 11 da aka sace a wurare daban-daban.
Ya kara da cewa, an kama wani da ake zargin mai samar da ƙwayoyi ne ga ‘yan ta’addan ISWAP a kusa da titin Bukarti.