Atiku Ya Yi Allah-Wadai da Kashe Kashen Kwara, Katsina Da Binuwe

[ad_1]

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi kakkausar suka kan kisan gillar da aka yi a wasu sassan jihohin Kwara, da Katsina da Binuwe, yana mai cewa lamarin ya nuna cewa Nijeriya ta “zama filin kisa.” Atiku ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta a ranar Alhamis.

Ya zargi gwamnati da gaza cika muhimmin nauyinta na kare rayukan jama’a, yana mai cewa yawan hare-haren da ake kaiwa na nuna mummunar gazawarsu a jahohi, musamman wajen kare marasa ƙarfi. Ya ƙara da cewa, yin Allah-wadai bayan an riga an binne gawawwaki ba su isa ba.

  • HOTUNA: Ɗan Ganduje Ya Ziyarci Kwankwaso A Kano
  • 2027: Atiku Ya Yi Ganawar Sirri Da Shugabannin Jam’iyyar ADP Kan Jita-Jitar Takarar Obi Da Kwankwaso

Atiku ya jaddada cewa tsaro dole ne ya zama na rigakafi kuma mai tsari, ba wai na mayar da martani bayan aukuwar hari ba.

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da jama’a ke ci gaba da nuna fushin kan kisan da aka yi a ƙauyen Woro da ke Ƙaramar Hukumar Kaiama a Jihar Kwara, inda aƙalla mutane 162 suka mutu sakamakon harin ’yan bindiga. Hukumar agaji ta Red Cross ta Nijeriya ta tabbatar da adadin mamatan, tana mai cewa har yanzu ana ci gaba da aikin bincike da ceto.

Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana harin a matsayin mummunan yunƙurin ƙungiyoyin ta’adda, tare da bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da tura rundunar sojoji ƙarƙashin Operation Savannah Shield domin kai hare-haren ramuwar gayya kan masu aikata laifin. Shaidu sun ce ’yan bindigar sun shiga ƙauyen da yamma, suna ƙone gidaje, da shaguna da masarauta, yayin da da dama suka rasa ransu yayin da suke ƙoƙarin tserewa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *