INEC Ta Yi Watsi Da Shugabancin PDP Da Turaki Ke Jagoranta
[ad_1]
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa ta ƙi amincewa da Kwamitin Aiki na Ƙasa da Kabiru Turaki ke jagoranta na Jam’iyyar PDP, sabida cewa, har yanzu akwai koke kan shugabancin jam’iyyar a kotu.
A cikin wata sanarwa mai kwanan wata 22 ga Disamban 2025, wacce Sakatariyar INEC, Dr. Rose Oriaran-Anthony, ta sanya wa hannu, hukumar ta ce, ba za ta iya bin buƙatun amincewa ko wallafa jerin sunayen shugabannin da aka zaɓa a Babban Taron Jam’iyyar PDP da aka yi a Ibadan a ranakun 15-16 ga Nuwamba, 2025 ba.
Hukumar ta fayyace cewa, akwai shari’o’in da ba a warware su ba game da takaddamar shugabancin cikin gida na PDP.
INEC ta jaddada cewa, amincewa da shugabancin wani ɓangare yayin da lamarin har yanzu yana ƙarƙashin shari’a bai dace ba.
[ad_2]
Source link