Ƴansandan Abuja Sun Nemi NLC Ta Dakatar Da Zanga-zangar  Da Ta Shirya Gobe

[ad_1]

Rundunar ƴansandan Babban Birnin Tarayya (FCT) ta buƙaci ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), reshen FCT, da ta yi la’akari tare da sake tsara wa ko dakatar da zanga-zangar lumana da ta shirya gudanarwa a ranar Talata, 3 ga watan Fabrairu, 2026, bisa rahotannin sirri da ke nuna yiwuwar wasu ƙungiyoyi da aka haramta su kutsa cikin zanga-zangar domin tayar da tarzoma.

A wata sanarwa da kakakiyar rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar a ranar Litinin, ta jaddada cewa duk da girmama haƙƙin ’yan ƙasa na taruwa cikin lumana kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, akwai sahihan bayanan asiri da ke nuna cewa wasu ɓata gari na shirin amfani da damar zanga-zangar domin haddasa rikici.

  • Hukumar FCTA Ta Fatattaki Mabarata 607 Daga Titunan Abuja
  • Wani Direba Da Ya Buge Mai PoS Har Lahira Ya Tsere A Abuja

“Rundunar na girmama haƙƙin taruwa cikin lumana da kundin tsarin mulki ya tanada,” in ji SP Adeh a wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Facebook. “Sai dai rahotannin sirri sun nuna cewa wasu ƙungiyoyi da aka haramta da wasu mutane na shirin kutsa kai ciki su kwace akalar zanga-zangar, wanda hakan na iya barazana ga zaman lafiya da tsaron jama’a.”

Ta bayyana cewa an ba da shawarar ga NLC ta sake tsara zanga-zangar ne domin kare lafiyar jama’a da kauce wa yiwuwar taɓarɓarewar doka da oda a babban birnin tarayya.

“Domin kare lafiyar jama’a, Rundunar ’Yansandan FCT ta shawarci masu shirya zanga-zangar da su yi la’akari da sake tsara ta, don hana taɓarɓarewar doka da oda da kuma kare rayuka, da dukiya da haƙƙin sauran mazauna FCT,” in ji sanarwar.

SP Adeh ta kuma tabbatar wa al’umma cewa rundunar na ci gaba da jajircewa wajen kare dukkan ayyukan da doka ta amince da su, tare da kira ga mazauna FCT da su ci gaba da haɗa kai da hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *