Laftanar ɗin soji ya ɓace bayan harin ’yan ta’adda a Borno
An kashe wani jami’in tsaron daji, yayin da aka ayyana wani laftanar na Sojan Najeriya a matsayin wanda ya ɓace, sakamakon wani mummunan hari da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai a ƙauyen Kawuri da ke Ƙaramar Hukumar Konduga a Jihar Borno.
Wata majiya daga cikin jami’an tsaro da ta tabbatar da lamarin ta ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:40 na daren ranar Alhamis.
A cewar majiyar, ‘yan ta’addan masu yawan gaske sun mamaye yankin ne ɗauke da muggan makamai ciki har da bindigogin harbo jiragen sama, inda suka kai farmaki kan wani sansanin sojin Najeriya da ke cikin al’ummar.
Majiyar ta ce harin ya yi sanadiyyar ɓacewar laftanar ɗin sojan a yayin artabu mai tsanani tsakanin sojoji da ‘yan ta’addan.
Ta ƙara da cewa an kashe wani jami’in tsaron gandun daji, wanda ɗaya ne daga cikin jami’an da gwamnatin tarayya ta tura kwanan nan domin tallafa wa sojojin Najeriya a yaƙin da ake yi da ta’addanci.
“Sun kuma ƙona wasu sassan sansanin sojojin kafin su tsere zuwa tsaunukan da ke kewaye da yankin,” in ji majiyar.
A ‘yan kwanakin nan dai, mayaƙan Boko Haram sun ƙara tsananta hare-hare a wasu sassan Jihar Borno, inda ake zargin suna amfani da manyan makamai, har da jiragen yaƙi marasa matuƙa.
Kazalika, an ruwaito cewa ‘yan ta’addan sun kai wani hari a yankin Sabon Gari kwanan nan, inda suka riƙa buɗe wuta da makamai na zamani, lamarin da ya janyo asarar rayuka a tsakanin sojoji da fararen hula.
Duk da ƙoƙarin da aka yi, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu cikakken bayani daga hukumomin soji dangane da lamarin ba.