Karuwar Mace-mace A Asibitocinmu Sakamakon Sakacin Jami’an Lafiya
[ad_1]
Asibitoci a Nijeriya, musamman ma na gwamnati, akwai korafe-korafe da dama a kan rashin kula na ma’aikatan lafiya, lamarin da ya kai ga mutuwar marasa lafiya lokaci bayan lokaci.
Abin takaici, a cikin shekarun da suka wuce, raunin sa ido da rashin bin diddigin gaskiya da kuma rashin gamsuwa na hukumomi, sun ba da dama wajen ci gaba da tabarbarewar wadannan al’amura tare da ci gaba da azabtar da marasa lafiya.
- Gobara Ta Hallaka Mutum 2, Ta Lalata Dukiya Ta Biliyan 1.59 A Bauchi
- CGI Babandede Mai Ritaya A Mizanin Kyawawan Halaye Da Kwazon Aiki
Jerin sakacin da ake samu:
A asibitocin gwamnati na Nijeriya, akwai yanayi na sakaci, wanda ke haifar da mace-mace sakamakon rashin yin rigakafin kamuwa da cututtukan da ke addabar iyalai daban-daban masu tarin yawa.
Daga kan matsalolin gaggawa wadanda ba a cika kula da su ba zuwa ga rashin kwararrun ma’aikata da kuma ka’idojin likitanci, gazawar tsarin na ci gaba da cutar da marasa lafiya, musamman mata da yara kanana.
A cikin ‘yan makwannin nan, raunin da aka samu ta fuskar tsarin kiwon lafiya a Nijeriya, ya haifar da samun mace-mace masu ratsa zuciya da ke da nasaba da rashin kulawar likitoci. Wadannan bala’o’i suna nuna gazawar tsarin tun daga tushe, musamman ga masu karamin karfi da kuma ma’aikatan da suke yin aiki tukuru.
Babu shakka, wannan matsala na ci gaba da lakume rayukan wadanda ba su ji ba; ba su gani ba, musamman a tsakanin mata da yara kanana wadanda suka dogara kacokan a kan wannan tsari na kiwon lafiya.
Mutuwar Dan Chimamanda
Mummunar mutuwar da dan Chimamanda Ngozi Adichie ya yi na baya-bayan nan, ya haifar da firgici a dukkanin fadin Nijeriya, wanda ya sanya tsarin kula da lafiya na kasar ke cikin tsananin bincike.
Mutuwar Nkanu Nnamdi, dan wata 21, wanda da ne ga fitaccen marubucin duniyar nan, Dakta Ibara Esege, ta zama abin kwatance a cikin muhawarar kiwon lafiyar Nijeriya.
Nkanu ya rasu ne a farkon watan Janairu, bayan duba shi tare da yi masa magani a wani asibitin Legas. Iyayensa sun yi zargin cewa, ba shi magunguna barkatai da kuma rashin isassun sa ido da bayar da agajin gaggawa, sun taimaka wajen mutuwarsa, lamarin da ya haifar da cece-kuce, inda suka zargi asibitin da ma’aikatan da saba wa aikinsu na bayar da kulawar da ta kamata.
A cikin sanarwar da ta fitar, Adichie ta yi karin bayani kan lamarin, inda ta zargi asibitin da rashin kula da lafiya, inda ta kara da cewa; rashin kulawar da suka samu ce ta kai ga mutuwar danta.
Ta ci gaba da cewa, an kai dan nata Asibitin Euracare, domin yi masa gwajin MRI, daga nan sai aka kwantar da shi, wanda sam-sam bai samu irin kulawar da ta dace ba, tun bayan yi masa wata allura ta ‘propofol’, baki-daya jikinsa ya rikice.
Kazalika, ta bayyana cewa danta, “babu abin da zai hana danta rayuwa, ba don kai shi wannan asibiti na Euracare ranar 6 ga Janairu da suka yi ba”, domin duba lafiyarsa. Adichie ta bayyana cewa, danginta sun kasance a Legas domin hutun Kirsimeti lokacin da dan nata ya kamu da wannan ciwo da kyautata zaton da farko sanyi ne, wanda daga baya “ya koma zuwa wata cuta mai tsanani.”
Shahararren marubucin ya ce: “Mun je Legas ne domin bikin Kirsimeti, Nkanu ya fara tunanin sanyi ne kawai, amma ba da jimawa ba sai ya koma wani ciwo mai tsanani, inda aka kwantar da shi a asibitin Atlantis.
“Washegarin 7 ga watan Janairu, zai yi tafiya zuwa Amurka tare da rakiyar likitocin balaguro. Sannan wata tawaga a Johns Hopkins na jiran tarbarsa a Baltimore.”
A cewarta, Asibitin Atlantis ya tura su asibitin Euracare, “wanda aka ce shi ne wuri mafi kyau wajen gudanar da ayyukan lafiya. Da safiyar ranar 6 ga wata, mun tashi daga Asibitin Atlantis zuwa Euracare, inda Nkanu yake dauke a hannun mahaifinsa.
“An gaya mana cewa, zai bukaci a kwantar da shi don hana shi yin motsi a lokacin gwajin MRI. Ina jira a wajen dakin tiyata, yayin da na ga mutane, ciki har da Dakta M, suna shiga cikin dakin tiyatar, inda nan da nan kuma na fahimci cewa, lallai wani abu ya faru.”
Adichie ta ce, daga baya sai aka fada mata cewa; lallai an yi wad an nata allurar da ta zarce ka’ida, inda ta ce; “Ba da jimawa ba, sai Dr. M. ya fito ya ce da ni, an yi wa Nkanu allurar propofol da ta zarce ka’idar da ya kamata a yi masa.”
Ta kara da cewa, daga baya an sanya wa dan nata na’urar kara numfashi, inda aka bayyana mata cewa; bayan da ya kamu da wannan cuta, sannan kuma ya samu bugun zuciya.
“Amma ba zato ba tsammani, sai ga Nkanu a kan na’urar kara numfashi, an sanya shi a cikin ICU, abu na gaba da na ji shi ne ya kamu da cutar bugun zuciya, wanda duk wadannan ba su taba faruwa da shi ba, bayan wasu sa’o’i kuma, Nkanu ya ce ga garinku,” in ji ta.
Adichie ta kuma yi zargin cewa, sam danta bai samu kulawa ba bayan kwantar da shi, inda kuma ta bayyana abin da likitan ya yi a matsayin rashin kulawa.
Da take yin kuka, ta ce; “Ba a sa ido a kan Nkanu ba, bayan yi masa wannan allura ta barci da ta zarce ka’ida. Likitan da kansa ya dauki Nkanu a kafadarsa ya shiga da shi dakin tiyata, don haka babu wanda ya san ainihin lokacin da Nkanu ya fita daga hayyacinsa.
Danta ya kasance “ba shi da lafiya, amma kuma yana cikin hayyacinsa, wanda kuma yana shirin yin tafiya ne washegari”, abin da ta bayyana a matsayin “muhimmin tsari,” amma ta rasa shi babu zato babu tsammani.
Da yake mayar da martani kan zargin rashin kula da lafiyar yaron, hukumar gudanarwar asibitin, a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta mika matukar juyayinta ga Chimamanda Ngozi Adichie da iyalanta kan rasuwar dan nasu, tare da amincewa da “asara mai girma da ba za a iya misaltuwa ba.”
Asibitin ya fayyace abin da ya bayyana a matsayin kuskure da kuma ikirarin da ake yi a shafukan sada zumunta, yana mai nuni da cewa; mutuwar ta biyo bayan rashin kulawar likitoci.
Asibitin ya kuma bayyana cewa, cibiya ce da ta shahara wajen samar da hadadden tsarin kula da lafiya, karkashin jagorancin kwararrun likitocin duniya. Ya bayyana cewa, yaron wanda ke fama da matsanancin rashin lafiya, an tura shi wurinta domin aiwatar da hanyoyin bincike, bayan ya samu kulawar asibitoci biyu na yara mako guda da ya gabata.
“Bayan isowar tawagar likitocinmu, nan da nan muka bayar da kulawa daidai da ka’idojin asibiti da aka kafa da kuma ka’idojin kiwon lafiya na duniya,” in ji sanarwar.
Asibitin Euracare ya kara da cewa, a yayin kula da mara lafiyar, tawagarsa sun yi aiki tare da kungiyoyin likitoci na waje, kamar yadda iyali suka ba da shawara, sannan kuma sun tabbatar da cewa; an ba da dukkannin wani tallafi da asibitin ya kamata ya bayarr. Duk da wannan kokari, majinyacin ya mutu kasa da sa’o’i 24 bayan an gabatar da shi a asibitin.
[ad_2]
Source link