Fashewar wani abu ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya da jikkata wasu a kudancin Iran

[ad_1]



Kafofin yaɗa labarai a Iran sun ruwaito cewa mutum ɗaya ya mutu, yayin da wasu suka jikkata bayan fashewar wani abu a wani gini a birnin Bandar Abbas a kudancin ƙasar.

Har yanzu ba a bayyana ainihin abin da ya jawo fashewar ba.

Sai dai wasu saƙonni da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun yi iƙirarin cewa an kai hari ne kan kwamandan sojin ruwa na rundunar dakarun juyin juya halin Iran.

Amma wani jami’i daga kamfanin dillancin labaran ƙasar ya musanta wannan iƙirari.

Bidiyon da aka ɗauka a wajen ya nuna cewa aƙalla hawa biyu na ginin sun lalace sosai.

A wani labari na daban, kafar yaɗa labaran gwamnati ta ce wasu mutane huɗu sun mutu sakamakon fashewar wani abu birnin Ahvaz.

Duk da haka, wata majiya daga hukumomin ƙasar ta ce duka fashewar abubuwan biyu sun faru ne sakamakon fashewar tukunyar gas.

Waɗannan abubuwa na faruwa ne a daidai lokacin da ake zaman ɗar-ɗar tsakanin Iran da Amurka, inda ake zargin Iran da kashe masu zanga-zanga, tare da rahotanni da ke cewa shugaban Amurka Donald Trump na duba yiwuwar ɗaukar matakan kai wa Iran hari.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *