An hana ’yan jarida shiga wajen bikin yaye ɗalibai a Jami’ar ABU
[ad_1]
Jami’an tsaro a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya, sun hana ’yan jarida shiga wajen bikin kammala karatu karo na 45 na jami’ar da aka gudanar a ranar Asabar.
An hana wakilan kafafen watsa labarai da dama shiga dandalin Mamman Kontagora Square, inda ake gudanar da bikin.
Daga cikin kafafen da abin ya shafa akwai Hukumar Gidan Rediyon Tarayya (FRCN), Daily Trust, Aminiya, Hukumar Dillancin Labarai ta Ƙasa (NAN), Kaduna State Media Corporation (KSMC), Nagarta Radio, NTA Zariya da sauransu.
Wani jami’in tsaro a jami’ar da ya bayyana sunansa da Mista C.K. ya ce yana bin umarnin Babban Jami’in Tsaron Jami’ar, Malam Ashiru Zango.
“An umarce mu da mu hana ’yan jarida shiga sai sun samu izini daga Shugaban Jami’a,” in ji shi.
Ya ce hakan ya faru ne duk da cewa ’yan jaridan sun nuna katunan shaidar tantancewa da jami’ar ta ba su.
’Yan jaridan da abin ya shafa sun nuna rashin jin daɗinsu, inda suka ce tuni an tantance su tare da ba su izinin halartar bikin.
Shugabancin Ƙungiyar ’Yan Jaridu ta Nijeriya (NUJ), ya shiga tsakani, tare da ƙoƙarin tuntuɓar Daraktan Harkokin Yaɗa Labarai na jami’ar, Malam Auwalu Umar.
Umar, ya ce zai shiga lamarin domin ganin an bai wa kafafen watsa labarai damar shiga wajen bikin.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wani ci gaba da aka samu, yayin da ’yan jarida da dama suka bar wajen taron sakamakon rashin samun damar shiga.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link