An ɗauke wuta a babban birnin Greenland

[ad_1]



Rahotanni na cewa an ɗauke wutar lantarki a Nuuk, babban birnin Greenland, a ƙarshen mako bayan wata iska mai ƙarfi ta lalata layin wutar lantarki.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na dare ranar Asabar, inda birnin da ke da kusan mutane 20,000 ya fada cikin duhu.

Sai dai Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa wutar lantarkin ta fara dawowa ne a wasu yankuna bayan kusan sa’o’i uku da ɗauke wutar.

Kamfanin wutar lantarki na gwamnati, Nukissiorfiit, ya bayyana cewa iska mai ƙarfi ce ta haddasa matsalar, kuma ana ƙoƙarin dawo da wuta ta hanyar tashar wutar gaggawa.

Haka kuma, matsalar ta shafi intanet, inda rahotanni suka nuna raguwar sadarwa a faɗin birnin Nuuk.

Lamarin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan gwamnatin Greenland ta fitar da wata takarda da ke ba mazauna yankin shawarwari kan yadda za su shirya idan aka samu matsalar gaggawa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *