Zaɓen Cike Gurbi: An taƙaita zirga-zirga a ƙananan hukumomi 2 a Kano

[ad_1]



Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga na awanni 18 a Ƙaramar Hukumar Birni da Ungogo gabanin zaɓen cike gurbi na majalisar dokokin jiha da za a gudanar a ranar Asabar.

Rundunar ta ce wannan na cikin matakan tsaro da ta ɗaukar domin tabbatar da an gudanar da zaɓen cikin lumana.

Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne,ya bayyana hakan a madadin kwamishinan ’yan sandan jihar.

Ya ce umarnin zai fara aiki daga ƙarfe 12 na dare zuwa 6 na yammancin ranar 21 ga watan Fabrairu 2026, kuma ya shafi motoci, adaidaita sahu da babura.

Sai dai ya ce motoci kamar na asibiti, motar kashe gobara, da na jami’an zaɓe da masu sanya ido da aka tantance za a ba su damar zirga-zirga.

Rundunar ta za a ƙyale masu kaɗa ƙuri’a, wakilan jam’iyyu da na INEC da aka tantance domin zuwa wajen zaɓe.

Kiyawa, ya ce rundunar tare da sauran hukumomin tsaro sun ɗauki dukkanin matakan da suka dace domin tabbatar da zaɓe cikin lumana.

Rundunar ta haramta ɗaukar makamai da nuna alamun jam’iyyun siyasa a wuraren zaɓe.

Rundunar ta ce ba za a bar duk wanda ya sanya tufafi ko ya riƙe kayan da ke ɗauke da tambarin jam’iyya ya shiga wajen zaɓe ba.

Kiyawa ya ce, an hana ƙungiyoyin tsaro na jiha kamar ’yan sa-kai, Hisbah da hukumomin kula da zirga-zirga aiki a wuraren zaɓe.

Ta jaddada cewa hukumomin tsaro da kundin tsarin mulki ya amince da su kaɗai ne za su kula da tsaro a wuraren zaɓen.

Zaɓen cike gurbin ya biyo bayan rasuwar ’yan majalisar jihar guda biyu, Aminu Sa’ad Ungogo da Sarki Aliyu Daneji, waɗanda dukkaninsu ’yan NNPO ne, kuma sun rasu a rana ɗaya a watan Disamban 2025.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *