An Sace Ƴan Kasuwa Huɗu A Wani Sabon Hari A Kaduna
[ad_1]
Aƙalla ƴan kasuwa huɗu ne aka sace a kan hanyarsu ta komawa gida bayan sun kammala siyayya a kasuwar Maro da ke ƙaramar hukumar Kajuru a Jihar Kaduna. Wata majiya ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Juma’a, lokacin da masu garkuwa suka yi musu kwanton bauna a kan hanyar Maro zuwa Kajuru.
Wannan sabon harin ya biyo bayan sace fiye da masu ibada 100 a yankin Kurmin Wali, a ƙaramar hukumar Kajuru, a makon da ya gabata, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin fargaba yayin da hukumomi ke ci gaba da ƙoƙarin ceto waɗanda abin ya rutsa da su.
- Sace Masu Ibada: Ashiru Ya Caccaki Gwamnatin Kaduna Kan Rashin Iya Shugabanci
- Gwmantin Kaduna Ta Tabbatar Da Sace Masu Ibada 177 A Kajuru
Da yake magana da manema labarai ta wayar tarho, Shugaban reshen Arewa na Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN), Fasto John Hayab, ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani kan sabon sace-sacen ba, amma ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa kan masu aikata laifuka. Ya ce, “Muna rokon gwamnati ta nuna ƙarfin iko wajen bibiyar ƴan ta’addan da ke neman haddasa rikici a jihar.”
A wani ɓangare kuma, wani babban jami’in gwamnati da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce yana jiran cikakken rahoto daga hukumomin tsaro kafin ya fitar da matsayar hukuma. Ya bayyana cewa ya riga ya tuntuɓi shugabannin tsaro a jihar domin samun sahihan bayanai.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴansandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, bai yi nasara ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, domin bai amsa kiran waya ko biyo baya ba. Ana sa ran ƙarin bayani daga hukumomi a nan gaba.
[ad_2]
Source link