An kama mai yi wa jami’an FRSC sojan gona yana ƙwace babura a Kano
Hukumar Kiyaye Haɗura ta Najeriya (FRSC), ta sanar da cafke wani mutum da take zargin yana yi mata sojan gona yana ƙwace babura a sassa daban-daban na Jihar Kano.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar reshen Jihar Kano, Abdullahi Labaran, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce, wanda ake zargin mai suna Abdullahi Ali, ɗan ƙauyen Bela ne na ƙaramar hukumar Ungoggo da ke Jihar Kano wanda aka cafke a ranar 19 ga Janairun 2026, bayan samun ƙorafe-ƙorafe da dama daga jama’a.
Labaran ya ce ƙorafe-ƙorafen sun shafi mutanen da ke yi wa jami’an FRSC sojan gona domin ƙwace babura ba bisa ƙa’ida ba, inda suke fakewa da cewa suna aikin sintiri ne.
BBC ya ruwaito cewa binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin yana amfani da ƙarfi wajen ƙwace babura yayin da yake tafka ta’asar ta sojan gona, inda ake zargin an sace wasu daga cikin baburan da aka ƙwace.
Ya ƙara da cewa an samu lasisin tuƙi na bogi a hannun wanda ake zargin lokacin da aka kama shi, lamarin da ke nuna amfani da shaidar ƙarya wajen aikata laifin.