Ɗalibin Jami’a Ya Hallaka Kansa Har Lahira A Neja
[ad_1]
Ana zargin wani ɗalibin aji uku a Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU), Lapai da ke Jihar Neja, mai suna Kelvin Danlami, da kashe kansa.
An same shi a ɗakinsa da safiyar ranar Talata.
- Tinubu Da Kwankwaso Za Su Gana Yayin Da Siyasar Kano Ta Ɗauki Sabon Salo
- AFCON 2025: Dalilin Da Ya Sa Super Eagles Ba Ta Jira Bikin Karɓar Kyautar Tagulla Ba – NFF
Rundunar ‘yansandan Jihar Neja ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta, Wasiu Abiodun.
‘Yansanda sun ce an gano ɗalibin ne a ɗakinsa da safiyar ranar.
Marigayin, ɗalibi ne a fannin Kimiyyar Kwamfuta a Jami’ar mallakar jihar.
Wasu majiyoyi sun ce yana fuskantar matsalar biyan kuɗin haya, amma babu wani tabbaci game da hakan zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
[ad_2]
Source link