Nijeriya Ta Koma Matsayi Na 26 A Jadawalin Iya Taka Leda Na Hukumar FIFA
[ad_1]
Tawagar kwallon kafa ta Nijeriya Super Eagles tayi nasarar haurawa zuwa matsayi na 26 a jadawalin iya taka leda a kwallon kafa da hukumar kwallon kafa ta Duniya (FIFA) ta fitar, wannan na zuwa ne bayan kokarin da Super Eagles sukayi a gasar da aka kammala a kasar Morocco inda suka kare a matsayi na Uku.
Tawagar, karkashin jagorancin Koci Eric Chelle, ta samu nasara shida, inda tayi rashin nasara sau daya kacal a wasanni bakwai da ta buga a gasar AFCON ta bana, Super Eagles ta samu maki 1581.55 a watan Janairun 2026, inda ta samu karin maki 79 daga maki 1502.46 da take dashi a watan Disamban 2025.
Hakazalika yanzu Super Eagles ke zaune a matsayi na 3 a iya taka leda a nahiyar Afirika, wanda ke nufin ta sha gaban kasar Algeria a jadawalin, kasashen Morocco da Senegal ne kadai ke saman Nijeriya a sabon jadawalin da FIFA ta fitar, Yanzu Ita Ce Ƙasa Ta Uku A Afirka Mafi Girma, Tana Baya.
Duk da rashin nasara a wasan karshe na gasar cin kofin kasashen nahiyar Afirika da Morocco tayi, amma ta cigaba da rike matsayinta na 1 a nahiyar Afirika inda take matsayi na 8 a jadawalin Duniya, Senegal wadda take matsayi na 2 a nahiyar Afirika ta samu nasarar zama ta 12 a jadawalin Duniya.
[ad_2]
Source link