Sin Na Daga Cikin Manyan Abokan Cinikayya 3 Na Zimbabwe A Shekarar 2025


Hukumar bunkasa cinikayya ta kasar Zimbabwe (ZimTrade), ta ce kasar Sin ce kasa ta uku cikin kasashen da Zimbabwe ke sayar da kayayyaki, inda ta dauki kaso 16.9 na kayayyakin da Zimbabwe ke fitarwa zuwa kasashen waje a watanni 11 na farkon shekarar 2025.

A cewar shugaban ZimTrade Allan Majuru, akwai damarmakin samun ci gaba ta hanyar hadin gwiwar dake akwai tsakanin gwamnatocin kasashen biyu domin bunkasa cinikayyar muhimman kayayyakin kasar kamar lemu da avocado.

Ya ce, Zimbabwe na ta fadada fitar da kayayyakinta na gona zuwa Sin, inda kasashen biyu suka rattaba hannu kan jerin shirye-shiryen fitar da kayayyaki da suka hada da lemu da avocado da blueberries.

A cewar hukumar ZimTrade, abun da kasar ta samu daga fitar da kayayyaki daga watan Janairu zuwa na Nuwamban shekarar 2025 ya kai dalar Amurka biliyan 8.57, karuwar kaso 27 kan dalar Amurka biliyan 6.74 da aka samu a makamancin lokacin a shekarar 2024.

Cikin wata sanarwa da ZimTrade ta fitar a watan Oktoban shekarar 2025, Allan Majuru ya jinjinawa shirye-shiryen cinikayya da aka rattabawa hannu tsakanin kasashen biyu, wadanda suka bayar da damar fitar da amfanin gona na Zimbabwe zuwa katafariyar kasuwar kasar Sin. (FMM)



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *