ASUU Ta Yi Watsi Da Ƙarin Albashin Kashi 35, Ta Buƙaci A Bai Wa Jami’o’i Isassun Kuɗi

[ad_1]


Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta ƙi amincewa da shirin Gwamnatin Tarayya na ƙara wa malamai albashi da kashi 35, inda ta bayyana cewa wannan ƙarin ba zai magance matsalolin jami’o’i ba

Shugaban ASUU na yankin Legas, Farfesa Adesola Nassir, ya sanar da haka ne yayin wani taron ’yan jarida a LASUED.

Ya ce wannan tayi “ba shi da wani amfani” kuma zai ci gaba da barin malaman Nijeriya cikin jerin masu ƙaramin albashi a Afirka.

Nassir ya ce ƙarin bai daidaita da tsadar rayuwa ko nauyin aikin da malamai ke yi ba.

Ya kuma bayyana cewa har yanzu ba a magance muhimman matsalolin da ASUU ta daɗe tana kuka a kansu ba.

Ya bayyana yadda aka yi a yarjejeniyar 2009, inda Farfesa ke samun kusan dala $3,000 a kowane wata, amma kuɗin ya ragu saboda hauhawar farashi da ƙarancin kudin da ake bai wa jami’o’i.

ASUU ta gargaɗi gwamnati cewa idan ba a ɗauki mataki ba, al’amura za su ci gaba da taɓarɓarewa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *