Ƴan Nijeriya Sun Yi Amfani Da Litar Fetur Sama Da Miliyan 63.7 A Iya Watan Disamba
[ad_1]
Matatar man fetur ta Dangote ta samar da lita miliyan 32.02 na man fetur a watan Disamba 2025, daga cikin lita miliyan 63.7 da aka yi amfani da ita a gaba ɗaya Nijeriya. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata takardar da Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ta fitar.
Takardar ta bayyana cewa matatar Dangote ita kaɗai ta samar da kashi 71 cikin 100 na man da aka yi amfani da shi, inda aka yi hasashen matatar zata iya samar da samar da lita miliyan 50, wanda daga bisani aka iya samun iya lita miliyan 32, Wanda ahakan ya nuna yadda matatar ta samar da sama da kaso 50 na abinda ake hasashen zata samar.
- Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci
- Gasar Farashi A Ɓangaren Man Fetur Alheri Ne Ga ‘Yan Nijeriya —Masana
A ɓangaren matatun man fetur na Nijeirya kuwa (NNPC), rahoton ya nuna cewa dukkan matatun gwamnati guda uku sun ci gaba da kasancewa a rufe, ba tare da wani sabon ci gaba ba. Sai dai an ruwaito cewa an rika fitar da man da aka samar a baya daga matatar Port Harcourt, a matsakaicin lita 247,000 a rana, kafin ta tsaya da aiki a ranar 24 ga Mayu 2025.
Saboda ƙaruwar buƙata a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara, NNPC da wasu kamfanoni sun shigo da lita miliyan 42.2 na man fetur a rana, domin cike giɓin bukatar da ta kai lita miliyan 72.4 a kasuwar cikin gida.
Rahoton ya ƙara da cewa an ba da lasisin sabuwar matatar man fetur guda ɗaya, yayin da matatar Waltersmith (Train 2) ta kammala shirye-shiryen fara aiki, kuma ana sa ran za a fara shigar da albarkatun mai a kasuwa cikin wannan watan na Janairu 2026.
[ad_2]
Source link