Yawan Motoci Masu Aiki Da Sabbin Makamashi Da Sin Ta Sayar Ya Ci Gaba Da Zama Matsayin Farko A Duniya A 2025

[ad_1]

Bisa kididdigar da kungiyar masana’antar motoci ta kasar Sin ta bayar a yau Laraba an nuna cewa, a shekarar 2025, adadin motoci da kasar ta kera da ma yawan motocin da ta sayar duka sun wuce miliyan 34, wato ke nan sun karu da kaso 10.4% da 9.4% bisa na makamancin lokacin shekarar 2024, inda hakan ya sa kasar Sin ta ci gaba da zama matsayin farko a duniya a cikin shekaru 17 a jere.

Hakazalika, adadin motoci masu aiki da sabbin makamashi da kasar ta kera da ma na sayarwa duk sun wuce miliyan 16, wato ya karu da kaso 29% da 28.2% bisa na makamancin lokacin shekarar 2024.

Kana yawan sabbin motoci masu aiki da sabbin makamashi da aka sayar ya wuce kaso 50% bisa na dukkannin motocin da aka sayar a kasar, hakan ya sa shekaru 11 ke nan a jere da kasar Sin take kaiwa matsayin farko a duniya a fannin. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *