An Yi Bikin Murnar Kaddamar Da Shekarar Musayar Al’adu Da Cudanyar Jama’a Ta Sin Da Afirka A Afirka Ta Kudu
[ad_1]
An gudanar da bikin murnar kaddamar da shekarar musayar al’adu da cudanyar jama’a a tsakanin Sin da Afirka ta shekarar 2026 a birnin Pretoria, birnin fadar mulkin kasar Afirka ta Kudu a ranar 12 ga watan nan, wanda ofishin jakadancin Sin dake Afirka ta Kudu ya dauki nauyin shiryawa, kuma ya samu halartar jami’an siyasa na Afirka ta Kudu da wakilai daga kafofin watsa labarai da harkokin al’adu na Sin da Afirka ta Kudu kusan 100.
Bana shekara ce ta cika shekaru 70 da fara kulla huldar diflomassiya tsakanin Sin da kasashen Afirka. Yayin taron, Wu Peng, jakadan Sin a Afirka ta Kudu, ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, a cikin shekaru 70 da suka gabata, musayar al’adu da cudanyar jama’a a tsakanin Sin da Afirka sun samu babban sakamako. A halin yanzu, duniya na fuskantar manyan sauye-sauye da ba a ga irinsu ba cikin karni guda, kuma Sin da Afirka suna bukatar kiyaye adalci, karfafa hadin kai da taimakon juna, da habaka mu’amala da hadin gwiwa fiye da kowane lokaci a da. A wannan shekarar, ofishin jakadancin Sin dake Afirka ta Kudu yana da shirin gudanar da tarurruka kusan 20, ana fatan amfani da wannan dama don karfafa tushen hadin gwiwa da kuma hanzarta gina kyakkyawar makoma ta bai-daya ta Sin da Afirka a sabon zamani.
A nata bangaren kuwa, Mmapaseka Steve Letsike, mataimakiyar ministar kula da harkokin mata da matasa da nakasassu ta Afirka ta Kudu, ta ce dangantakar abokantaka tsakanin Afirka ta Kudu da Sin tana da dogon tarihi, kasashen biyu suna gudanar da hadin gwiwa mai zurfi a fannoni da dama kamar siyasa da tattalin arziki da zamantakewa da kuma kimiyya da fasaha.
Ta kuma ce zumunci mai kyau tsakanin bangarorin biyu ya dade da zama muhimmin tushe wajen habaka dangantakar Afirka ta Kudu da Sin da ma Afirka da Sin, kuma ci gaba da zurfafa musayar al’adu da cudanyar jama’a zai samar da sabon kuzari ga alakar kasashen biyu ta kud-da-kud. (Safiyah Ma)
[ad_2]
Source link